Gwamnatin Katsina za ta sayi baburan hawa 700 da motoci 20 don ƙarfafa tsaro a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin ta amince da haka a zaman majalisar zartarwa karo na 12 ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Raɗɗa a ɗakin taro na gidan gwamnatin jihar.

Majalisar ta kuma amince da sawo motoci na yaƙi guda takwas ƙirar Toyota Land Cruiser.

A hira da manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa, kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya ce waɗannan Baburan za su taimakawa jami’an tsaro wajan shiga maɓoyan ƴan ta’addan inda motoci ba za su iya shiga ba .

Haka kuma Dr Ɗanmusa ya ce ma majalisar ta amince da sauran kayan tsaro na zamani da jami’an tsaro za suyi amfani da su wajen tarwatsa sansani da sauran maɓoyan yan ta’adda a jihar.

kwamishinan ya bayyana cewa gwamna Dikko Raɗɗa dama ya faɗa a farin hawan sa kan mulki cewa ƙudirin sa na ɗaya na biyu da na uku duka duƙufa ne wajen samar da tsaro a jihar.

“Muna yaƙar ta’addanci a kowane ɓangarori na jihar,ba kuma zamu fasa sai mun dawo da zaman lafiya a jihar,”inji Dr Ɗanmusa.

Ya roƙi al’ummar jihar da su taya su addu’a da ba su goyon bayan wajen kawo ƙarshen ta’addanci a jihar.

By ukarofi