
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan jihar Neja Umaru Bago ya sauke ilahirin tawagar kwamishinoninsa.
Bago ya bayyana matakin ne yayin zaman majalisar zartarwar jihar a gidan gwamnatin jihar da ke Minna a yau Litinin.
A sanarwar da Sakataren yaɗa labaransa ya fitar, gwamnan ya yaba wa kwamishinonin bisa gudunmuwarsu ga ci-gaban jihar gami da musu fatan alheri a harkokinsu na nan gaba.
Sannan ya ce, ya dawo da Sakataren Gwamnatinsa (SSG), shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin da mataimakinsa, da wasu manyan jami’an gwamnatin nasa.
