Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugabannin Jam’iyyar PDP masu goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, sun gindaya sharuɗɗa kafin gudanar da taron gangamin ƙasa na jam’iyyar.
A taron da suka gudanar a Abuja ƙarƙashin ƙungiyar Eminent Leaders and Concerned Stakeholders of PDP, sun dage cewa Shugaban PDP na ƙasa ya ci gaba da kasancewa daga Arewa ta Tsakiya, kamar yadda aka tsara a rabon muƙaman taron 2021.
Haka kuma sun buƙaci a gudanar da sabbin tarurruka a jihohin Ebonyi da Anambra, da taron ƙananan hukumomi a Jihar Ekiti, tare da sake kiran sabon taron yankin Kudu maso Gabas.
Sun kuma nemi a mutunta sakamakon taron Kudu maso Kudu da aka yi a Kalaba, wanda kotu ta tabbatar da sahihancinsa.
Tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom, wanda ya karanta sanarwar bayan taron, ya gargaɗi cewa rashin bin waɗannan sharuɗɗa zai sa kowanne taron gangami da aka yi ya zama babu inganci, domin sahihan mambobin jam’iyya za su rasa damar shiga.
Taron ya samu halartar Wike, wasu tsoffin gwamnonin jihohi, ‘yan majalisar ƙasa na yanzu da na baya, da shugabannin PDP daga jihohi da dama.
Shugabannin sun jaddada cewa PDP dole ta tsaya kan adalci, gaskiya da bin doka idan har tana son dawowa matsayin jagorar adawa a Nijeriya.
