Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Neja Umar Mohammed Bago ya ce ya rushe kwamishinoninsa ne domin auna ƙoƙarin gwamnatinsa a rabin wa’adi.
A ranar Litinin ne gwamnan ya sauke duka kwamishinoninsa bayan zaman majalisar zartaswar jihar da ya guda a fadar gwamnatinsa.
To sai dai yayin tattaunawarsa da manema labarai, gwamnan ya ce akwai yiwuwar sake mayar da wasu cikin kwmaishinonin a wasu ma’aikatun na daban domin sake gwada sa’arsu.
Gwamnan ya ce gwamnati tana da faɗi don haka wasu za su sake komawa wasu fannonin.
“Wasu za su sake dawowa, yayin da wasu za su koma wasu ma’aikatun domin samun sabon tsari,” inji shi.
“Sun yi iya bakin ƙoƙarinsu: Wasu sun yi zarra, yayin da wasu suka yi ƙoƙarin a fannoninsu”, in ji shi.
Gwamnan ya kuma gode wa kwamishinonin nasa kan taimakon da suka bayar wajen ciyar da gwamnatinsa gaba.
