Faransa tana shirin haramta wa ƙananan yara amfani da soshiyal mediya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Alhamis ne ake yunƙurin haramta wa ƴan ƙasa da shekaru 15 a ƙasar Faransa amfani da kafafen sada zumunta yayin da ƴan 15 zuwa 18 kuma ake neman saka musu takunkumin amfani da su a lokutan dare.

Kwamitin majalisar dokokin ƙasar ya sanar da hakan a wani rahoto da ya fitar, bayan tattaunawa da iyalai, jagororin soshiyal mediya da sauran masu ruwa da tsaki a fannin.

Ofishin Shugaba Emmanuel Macron tuni ya bada goyon baya game da taƙaice wa ƙananan yara amfani da kafafen soshiyal mediya.

Hakan na zuwa ne shekara ɗaya da Australiya ta haramta wa ƴan ƙasa da shekaru 16 amfani da soshiyal mediya a ƙasar.

Shugaban kwamitin majalisar, Arthur Delaporte ya shaida wa AFP cewa a shirye yake ya shigar da ƙara akan TikTok bisa sanya rayukan masu amfani da shi cikin haɗari.

A watan Maris aka kafa kwamitin da nufin gudanar da bincike akan yadda TikTok yake tasiri akan ƙananan yara bayan wani ƙorafi da iyalan gida bakwai suka yi na zargin manhajar da sanya ababe masu kwaɗaitar da yara cutar da kansu ko ma kai su ga kashe kansu a wasu lokuta.

By Babaji