Kashi 31 na matan Nijeriya sun fuskanci cin zarafi – Ministar Mata

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministar mata a Nijeriya, Imaan Sulaiman Ibrahim ta ce kashi 31 na mata ‘yan shekaru 15 zuwa 49 sun fuskanci cin zarafi na zahiri irinsu duka, yayin da kashi 28 suka fuskanci cin zarafi kamar fyaɗe, aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu.

Ministar ta ce waɗannan bayanai na nuna zahiri irin halin da mata ke ciki a ƙasar, duk da irin ci gaba da ake samu wajen yaƙi da cin zarafin mata.

Ministar ta bayyana hakan ne a Abeokuta na jihar Ogun a jiya Talata, yayin ziyarar aiki da take kaiwa, inda ta ziyarci cibiyar kai ƙorafe-ƙorafen laifukan cin zarafi dake babban birnin jihar.

Imaan ta ce ya kamata al’umma su gane cewa cin zarafin mata ba matsala ce da ta shafi iya waɗanda ke fuskanta ba, sai dai matsala ce da ta shafi al’umma baki ɗaya, wadda kuma ke kawo tsaiko a zaman lafiya da zamantakewar iyali da kuma ci gaba.

Ministar ta ƙara da cewa, bayanan sun yi nuni da buƙatar dake da akwai na masu ruwa da tsaki su tashi tsaye tare da ɗaukar matakin bai ɗaya, domin magance matsalar.

By ukarofi