Tinubu ya yi tir da harin da Isra’ila kai wa ƙatar

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Nijeriya ta yi Allah-wadai da harin da Isra’ila ta kai a Doha, babban birnin ƙasar ƙatar, wanda ya shafi manyan shugabannin ƙungiyar Hamas, tana mai cewa matakin ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

Harin da aka kai a ranar Talata ya faru ne a yayin wani taro da aka yi domin tattaunawa kan shirin tsagaita wuta da Amurka ta yi wa Gaza.

Harin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida da suka haɗa da ɗan babban shugaban ƙungiyar Hamas Khalil al-Hayya, da daraktan ofishin al-Hayya, da masu gadi uku, da kuma wani jami’in tsaron ƙatar. Sai dai rahotanni sun ce manyan shugabanninta sun tsira daga harin.

ƙatar ce babbar mai shiga tsakani a tattaunawar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Hamas kuma gida ne ga sansanin sojin Amurka mafi girma a yankin, Al Udeid Air Base.

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Kimiebi Ebienfa, ya fitar a ranar Laraba, FG ta jaddada muhimmancin mutunta ikon ƙasa da kuma bin dokokin ƙasa da ƙasa.

Sanarwar ta ce, “Wannan ci gaban ya haifar da tambayoyi masu tsanani game da zaman lafiyar yankin da kuma fatan ci gaba da ƙoaarin diflomasiya da nufin warware rikicin Isra’ila da Falasɗinu.”

Gwamnatin Nijeriya ta kuma amince da daɗewar rawar da ƙatar ke takawa wajen inganta tattaunawa da sasantawa a yankin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Muna kira ga dukkan ɓangarorin da su yi tsayin daka, da kaucewa taɓarɓarewar tsaro, da kuma dagewa wajen yin aiki cikin lumana.”

Gwamnati ta jajanta wa waɗanda lamarin ya shafa tare da jaddada goyon bayanta ga shirye-shiryen da ke ƙarfafa rugujewa, tattaunawa da zaman lafiya mai ɗorewa.

Ma’aikatar ta kuma jaddada aniyar Nijeriya na haɗa kai da ƙasashen duniya ta hanyar Majalisar ɗinkin Duniya da sauran tarukan dandali domin ciyar da zaman lafiya da tsaro da bin doka da oda a yankin gabas ta tsakiya da ma sauran ƙasashen duniya.

Yaƙin Isra’ila da Falasɗinu a watan Oktoban 2023 ya fara kai wa Hamas harin ba-zata a kudancin Isra’ila, inda ya kashe mutane sama da 1,200 tare da yin garkuwa da sama da 200.

A wani mataki na ramuwar gayya, Isra’ila ta fara wani tsawaita yakin soji a Gaza, wanda ya haifar da ɓarna mai yawa da kuma zurfafa rikicin bil’adama.

By ukarofi