Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Spread the love

Liverpool da Manchester United na daga cikin manyan ƙungiyoyin da ke zawarcin matashin ɗan wasan baya na Ajax Aaron Bouwman, mai shekara 18.

ɗan wasan ƙasar Sifaniya kuma tsohon ɗan wasan baya na Manchester City Aymeric Laporte, mai shekara 31, yana jiran ya gano ko FIFA za ta amince da komawar shi zuwa Athletic Bilbao daga Al-Nassr bayan rashin yiwuwar hakan a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta bazara.

ɗan wasan tsakiya na Ingila Josh Brownhill, mai shekara 29, ya kammala gwajin lafiya a ƙungiyar Al-Shabab kuma yana shirin komawa ƙungiyar ta Saudiyya kyauta bayan ya bar Burnley a ƙarshen kakar wasan da ta gabata.

ɗan wasan Brazil Casemiro, mai shekara 33, an danganta shi da komawa Saudiyya amma Manchester United za ta iya ci gaba da riƙe shi har sai kwantiraginsa ya kare a bazara mai zuwa.

Inter Milan ta nuna sha’awarta a kan ɗan wasan Canada Jonathan David kafin ɗan wasan mai shekaru 25 ya koma Juventus a kyauta bayan ya bar Lille a bazara.

Manchester United na neman ɗan wasan Nottingham Forest Elliot Anderson, Arsenal ta samu ci gaba wajen tsawaita kwantiragin Bukayo Saka da William Saliba, kuma matashin ɗan wasan baya na Ajax yana jan hankalin mutane sosai.

Manchester United na zawarcin ɗan wasan Nottingham Forest da Ingila Elliot Anderson, mai shekara 22 a watan Janairu.

Arsenal na shirin tsawaita kwantiragin ɗan wasan Ingila Bukayo Saka da ɗan wasan bayan Faransa William Saliba, yayin da kwantaragin ‘yan wasan biyu, masu shekaru 24, zai kare a karshen kakar wasa ta 2026-27.

Mai tsaron ragar Kamaru Andre Onana, wanda ke daf da komawa Trabzonspor a matsayin aro, ya ki amincewa da tayin ƙungiyoyi da dama, ciki har da Monaco.

ɗan wasan bayan Manchester United da Netherlands Tyrell Malacia, mai shekara 26, zai iya zaman aro na tsawon kaka daya a kungiyar Eyupspor ta Turkiyya.

Real Madrid na neman dan wasan baya na Tottenham Micky van de Ven, ɗan wasan tsakiya na Manchester United Kobbie Mainoo yana son ya tashi a watan Janairu yayin da Arsenal za ta yi tunanin siyar da ‘yan wasanta biyu na gaba.

Real Madrid na sha’awar sayen ɗan wasan bayan Tottenham Micky van de Ven, mai shekara 24, amma Spurs za su yi tunanin sayar da ɗan wasan na Netherlands kan fan miliyan 70 kawai.

ɗan wasan tsakiya na Manchester United da Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, na iya neman tashi daga ƙungiyar don zuwa aro Napoli a watan Janairu idan bai samu ƙarin lokacin wasa a Old Trafford ba.

Arsenal za ta duba batun sayar da ɗan wasan gaban Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 28, da ɗan wasan gaban Belgium Leandro Trossard, mai shekara 30, a kasuwar musayar ‘yan wasa ta Janairu.

West Ham na tattaunawa don sake siyan golan Poland Lukasz Fabianski watanni biyu kacal bayan da ɗan wasan mai shekaru 40 ya bar ƙungiyar a lokacin da kwantiraginsa ya ƙare.

Atletico Madrid na zawarcin ɗan wasan Tottenham Rodrigo Bentancur da kwantiragin ɗan wasan tsakiyar Uruguay mai shekaru 28, zai ƙare a bazara mai zuwa.

Manchester United na fatan mai tsaron gida Andre Onana zai iya taka rawar gani a aron da ya je Trabzonspor a kakar wasa ta bana domin ta sayar da dan wasan na Kamaru mai shekaru 29 a kan kuɗi mai yawa a bazara mai zuwa.

ɗan wasan Manchester United ɗan ƙasar Ingila Sam Mather, zai iya barin kulob ɗin don komawa Turkiyya kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta kasar a matsayin aro ko kuma na dindindin.

Joao Mendes, dan Brazil kuma ɗan tsohon ɗan wasan Barcelona Ronaldinho, zai bar Burnley inda ake sa ran ɗan wasan mai shekara 20 da haihuwa zai koma kungiyar Hull City ta ‘yan ƙasa da shekara 21.

Manchester United ta shirya tsaf domin sayen ɗan wasan bayan Belgium Zeno Debast, mai shekara 21, a watan Janairu daga tsohon kulob ɗin kocinta Ruben Amorim na Sporting amma Arsenal da Aston Villa na cikin sauran ƙungiyoyin da ke zawarcinsa. 

By ukarofi