Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko ɗangote, ya yi alfahari da cewa direbobinsa suna samu fiye da waɗanda suka kammala karatun digiri da kuma ninki huɗu na mafi ƙarancin albashin Nijeriya.
Dangote ya bayyana haka ne a ranar Talata a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise, yayin da yake mayar da martani kan zargin da ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya (NUPENG) ta yi.
A baya-bayan nan ne ƙungiyar NUPENG ta zargi Dangote da Sayyu Aliu Dantata da aikata laifukan yaƙi da ƙungiyar. ƙungiyar ta yi iƙirarin cewa ’yan kasuwar na ƙoƙarin sanya hannun jari a Nijeriya wajen raba mai da iskar gas tare da danne haƙƙin ma’aikata.
A lokacin, ƙungiyar ta NUPENG ta ce mambobinta za su fara yajin aikin ne a faɗin ƙasar daga ranar Litinin 8 ga watan Satumba, domin nuna adawa da abin da ta bayyana a matsayin ayyukan da ƙungiyar ƙwadago ta ɗauka, da ke da alaƙa da tura sabbin motocin dakon iskar Gas (CNG) da matatar Dangote ta yi, domin rabon albarkatun man fetur kai-tsaye.
ƙungiyar ta NUPENG wacce ƙungiyar ta haɗa da direbobin tankar mai a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Williams Akhoreha da babban sakataren ƙungiyar Afolabi Olawale suka sanya wa hannu, ta yi zargin cewa ana tilastawa direbobin da aka ɗauka aiki da manyan motocin CNG da su sanya hannu a kan cewa ba za su shiga wata ƙungiya da ke da alaka da harkar mai da iskar gas ba.
A wancan lokacin ƙungiyar masu motocin haya ta Nijeriya wato NARTO ta bayyana goyon bayanta ga ƙungiyar NUPENG a ci gaba da gwagwarmayar da take yi da kamfanin Dangote.
Shugaban NARTO na ƙasa, Othman Yusuf, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ta yi watsi da shirin Dangote na rarraba albarkatun man fetur kai-tsaye, saboda rashin ɗorewa da kuma yiwuwar kawar da masu safara masu zaman kansu da ke amfani da motocin dakon mai sama da 30,000 a faɗin ƙasar nan.
Hakazalika, ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta goyi bayan ƙungiyar NUPENG, inda shugabanta Joe Ajaero ya zargi kamfanin Dangote da “cin zarafin ma’aikatan Nijeriya tare da yin watsi da haƙƙinsu na tsarin mulki.”
Da yake jawabi yayin hirar, Dangote ya ce ƙaddamar da manyan motocin bai hana kowa yin aikinsa ba, yana mai cewa batun ƙungiyar ta NUPENG ya zama na son rai.
A cewarsa, direbobinsa suna samun kusan sau uku zuwa huɗu na mafi ƙarancin albashi na ƙasa, inda wasu ke samun fiye da waɗanda suka kammala karatu.
Ya jaddada cewa manyan motocin da kamfaninsa ya ƙaddamar za su samar da guraben aikin yi 24,000, inda kowace babbar mota za ta tallafa wa kimanin mutane shida, inda ya ce bayan shekaru biyar na tuƙin mota ba tare da hatsari ba, direbobi na iya neman lamunin gidaje.
