Arsenal za ta taka rawar gani a gasar Zakarun Turai a bana – Valverde

Spread the love

Arsenal tana daga cikin ƙungiyoyin da za su iya lashe gasar Zakarun Turai a bana, inji kocin Athletic Bilbao, Ernesto Valverde.

ƙungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama za ta kara da Bilbao a filin wasa na San Mames a karawar farko a cikin rukuni a Champions League ranar Talata.

Gunners ta kai zagayen daf da ƙarshe a bara, wadda Paris St Germain ta yi waje da ita daga gasar ta Zakarun Turai.

Bilbao ta samu gurbin shiga Champions League a bana, bayan da ta kare a mataki na huɗu a teburin La Liga a kakar da ta wuce.

By ukarofi