Kocin Barcelona, Hansi Flick ya ce ya kamata hukumar ƙwallon kafar Sifaniya ta ɗauki matakin kula mafi inganci, bayan da Lamine Yamal ya ji rauni lokacin da yake buga wa kasar tamaula.
Mai shekara 18 ba zai buga wa Barcelona wasa da Valencia ranar Lahadi a gasar La Liga ba, watakila ba zai yi fafatawar da za ta fuskanci Newcastle United ba a makon gobe a Champions League.
Haka shima Frenkie de Jong ya ji rauni a lokacin da yake buga wa Netherlands tamaula, kenan shima ba zai buga wasan Valencia ba.
Sai dai Marc Bernal, mai shekara 18 zai koma taka leda, bayan wata 13 da ya sha jinya.
Barcelona za ta karɓi baƙuncin Valenci a filin wasa na Johan Cruyff ranar Lahadi, sakamakon da ake ta gyaran Camp Nou.
