Tsohon ɗan wasan bayan Barcelona Eric Abidal ya musanta jita-jitar mutuwarsa da ya karaɗe shafukan sada zumunta a wannan makon.
Labaran da aka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta sun nuna cewa Eric Abidal ya mutu ne bayan matsalar taɓarɓarewar lafiya da ya fuskanta sakamakon dashen hanta da aka yi masa a shekarar 2025, lamarin da ya sa dole ya fito ya bayyana cewa yana da rai.
A shekarar 2011 ce gwaji ya fara tabbatar da cewa Abidal mai shekaru 46 ya harbu da cutar dajin hanta. A cikin shekarar aka cire ƙarin daga hantarsa, kana aka masa dashe kafin ya koma ƙwallo a shekarar 2013.
Abidal ya wallafa a shafin dandallin sada zumuntar Instagram cewa, bai kamata a riƙa yaɗa wasu jita-jita ba, inda ya ce yana nan da rai da lafiya da shi da iyalansa.
A ƙungiyar Monaco Abidal ya fara sana’arsa ta ƙwallon ƙafa, daga nan ya garzaya Lille da Lyon duk a ƙasar Faransa, kafin ya koma Barcelona a shekarar 2007.
Bayan gwagwarmayar da ya sha da cutar daji, ya koma wasa a ƙungiyarsa ta Barcelona a shekarar 2013, amma ta sallame shi a ƙarshen kaka, inda ya koma Monaco, kafin ya ƙarƙare sana’arsa ta ƙwallon ƙafa a Olympiacos ta ƙasar Girka.
A yayin zaman sa a Barcelona, Abidal ya lashe kofuna 15 ciki har da na LaLiga 4 da na gasar zakarun nahiyar Turai 2.
Sau 67 ya buga wa tawagar ƙwallon ƙafar Faransa wasa.
Bayan ya yi murabus daga ƙwallon ƙafa ne ya koma Barca a shekarar 2018 a matsayin daraktan wasanni, ya bar aikin a shekarar 2020.
