Ɗan wasan tsalle-tsalle da guje – guje, Kayinsola Ajayi ya kafa tarihin zama ɗan Nijeriya na farko da ya kai wasan ƙarshe a gasar ƙasashen Duniya da ke ci gaba da gudana a birnin Tokyo na ƙasar Japan, bayan shafe shekaru 18.
Ajayi wanda ya yi tseren Gudun Mita 100, ya ƙarƙare a mataki na biyu a wasan dab da na kusa da na ƙarshe wato semi final, da ya kammala Gudun cikin daƙiƙa 9 da digo 93 a gasar ta ‘Tokyo World Championship’.
Nasarar ƙarewa a matakin na biyu, ya bashi damar zuwa wasan ƙarshe da ya sa ya zama ɗan Nujeriya na biyu da ya kai wasan ƙarshe a bangaren Maza, a tsawon shekaru 18, tun bayan Olusoji Fasuba a shekarar 2006.
ɗan wasan na jiran buga wasan ƙarshe a gaba da yake fatan lashe lambar Zinare a ƙasar ta Japan.
Sauran ‘yan wasan Afirka da suka tsallaka zuwa Mataki na gaba sun haɗa da Letsile Tebogo na Botswana sai Gift Leotlela da Akani Simbene dukkanin su daga Afirka ta Kudu.
