Tinubu ya ziyarci iyalan marigayi Buhari a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A jiya Juma’a Shugaba Bola Tinubu ya kai wa iyalan tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari ziyara a gidansu da ke Kaduna.

A yayin ziyayar, Tinubu ya samu tarba daga iyalan marigayin ƙarƙashin jagorancin maiɗakinsa, Hajiya Aisha Buhari.

Waɗanda suka masa rakiya sun hada da shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas.

Sauaran sun haɗa da gwamnonin Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq; Yobe, Mai Mala Buni; Borno, Babagana Zulum; Sakkwato, Ahmed Aliyu; ds Katsina, Dikko Raɗɗa.

Haka kuma akwai Ministan Kuɗi, Wale Edun; Atiku Bagudu, Ministan Kasafi; Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Matawalle; da Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu.

Da yake jawabi, Tinubu ya ce ba iya iyalan ke cikin jimamin rashin tsohon shugaban ƙasar ba, har ma da su a matsayinsu na jagorori da kuma ƴan ƙasa baki ɗaya.

Ya bayyana cewa, Shugaban ƙasar ya bar tarin ayyukan alkhairi, inda ya tabbatar da cewa za su cigaba da bin turbarsa wajen ciyar da ƙasa da al’umma gaba.

Da fari Shugaban Ƙasar ya halarci ɗaurin auren Nasirudeen Abdulaziz Yari, wato ɗan Sanata Abdulaziz Yari, da ke wakiltar Zamfara ta Yamma, wanda ya auri Safiyya Shehu Idris a Masallacin Sultan Bello da ke garin Kaduna.

By Babaji