2027: Kwankwaso ya bada sharaɗin koma wa APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagora a jam’iyyar NNPP, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana waɗansu sharuɗɗa da zu su iya janyo ra’ayinsa wajen sake shiga jam’iyya mai mulki ta APC.

Ya ce, wajibi ne a mutunta tafiyarsa ta Kwankwasiyya yayin da ya koma cikin kowane irin haɗakar siyasa.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi bakuncin Buhari Bakwana, tsohon mai bai wa tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje shawara kan harkokin siyasa tare da ƴan jam’iyyar APC daga ƙananan hukumomin Kano 44, a gidansa da ke Miller Road a Kano.

Kwankwaso ya tunatar da su cewa shi da wasu manyan jiga-jigai sun taka rawa wajen kafa APC a shekarar 2013, inda ya a yayin haka suka jure ɗaukar nauyin cin zarafi na siyasa a tafiyar.

“A ƙasar nan babu wanda zai gaya mani nauyin da muka ɗauka wajen samar da APC. Mu ne muka jagoranci kafa jam’iyyar, kuma mu ne gwamnoni bakwai da suka fara shelanta goyon bayanta. ICPC, EFCC, da ƴan sanda duk an yi amfani da su a kaina a lokacin, don kawai mu dakatar da shirinmu”, inji shi.

Jagoran na NNPP ya ƙara da cewa, duk wata tattaunawa kan haɗewa ko koma wa APC dole ne ta fayyace fa’idodi na zahiri ga jam’iyyarsa.

“Idan kuna neman mu koma APC, to ku gaya mana abin da NNPP za ta samu, muna da ƴan takarar gwamna a dukkan jihohi da cikkaken tsare-tsare a faɗin ƙasar, me za ku ba su idan muka shiga”, ya tambaya.

Kazalika, ya tuna da ɓacin ran da aka samu a ƙawance baya, inda ya zargi APC da PDP da cin amanar yarjejeniyar, yana mai bada misali da shekaru takwas na Buhari, wanda a cewarsa ba a ba su komai ba, koda shugaban yanki na PDP wanda suka nema.

By Babaji