Kano: An yi ayyukan raya ƙasa 140 a Ƙaramar Hukumar Bichi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Ƙaramar Hukumar Bichi ta Jihar Kano ce ta gudanar da ayyukan raya ƙasa da cigaban al’umma da adadinsu ya kai kimanin 140 a loko da saƙo na yankin.

Mataimakin shugaban karamar hukumar, Alhaji Abubakar Sabo Babangida Ɗan-Zabuwa ya faɗi haka yayin taron jin ra’ayoyin al’umma game da Kasafin kuɗin shekarar 2026 da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar.

Ɗan-Zabuwa, wanda ya yi magana a madadin shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya ce daga cikin ayyukan da aka aiwatar akwai; ginin makaranta mai ajujuwa biyu da sito da ofis a garin Ɗan-Zabuwa da Hayin Waya da Muntsira da Jallu da kuma ‘Yan-Bubdu.

“Akwai Empowerment da aka yi na mutum 300 da suka ƙunshi mazaɓu 11, sannan ya sai sababbin babura guda 24 wadanda aka raba wa DSS Education da kuma wasu muhimmai na jama’ar gari a mazabu 11, sannan akwai makarantu da karamar hukuma ta dau ‘yan asalin Karamar Hukumar Bichi domin su ci gaba da karo karatu. Wannan su ne kadan daga cikin abubuwan da mai girma shugaban Karamar Hukunar Bichi ya yi a wannan shekara”, inji shi.

Ya ƙara da cewa, an gina hanyar ruwa daga ‘Yarkasuwa zuwa Gwalalo da kuma wata a Santar Namama da katange ofishin Shiyyar Ilimina yankin. Sannan kuma da gyaran kananan asibitoci a Santar Komau da Kyauta da ‘Yangwarzo da Tinki tare da kuma sauran mazabu.

A nasa jawabin, shugaban sashen ƙididdiga na ƙaramar hukumar, Malam Isa Abba Umar ya yi bayani game da tsarin kasafin kuɗin da karamar hukumar za ta yi na shekara ta 2026.

“Gwamnati tana zaunawa ta tsara irin kasafin kuɗin da za ta samu da kuma inda za ta kashe su zuwa shekara, yanzu muna watan tara kafin nan da watan sha biyu an gama tsara kasafin kudi, na irin yanayin inda za a samo da kuma inda za a kashe su, a kan ayyuka bisa tsari.”

Daga nan ne sai Hakimin Bichi, Galadiman Kano, Alhaji Mannir Sanusi ya hori al’uma da shugabancin karamar hukumar, da su fito da ayyukan da za su taimaki al’umar Karamar Hukumar Bichi, a Kasafin Kudin Shekara ta 2026.

“Tsaro da harkar noma, wadannan abubuwan su muke nema a taimaka mana, kuma gwamnatin nan ta ce za ta taimaka mana”, kamar yadda jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi R/Lemo ta ruwaito.

By Babaji