Ribas: Ba zan yi katsalandan wajen naɗa kwamishinoni ba – Wike ga Fubara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Abuja Nyesom Wike ya bayyana cewa ba shi da burin bada zaɓinsa game da waɗanda za a bai wa muƙaman kwamishinoni a Gwamnatin Siminalayi Fubara, bayan dowawarta tun kafa dokar ta-ɓaci a jihar watanni shida da suka gabata.

Wike ya faɗi haka ne yayin hira akan maudu’in ‘Politics Today’ da gidan talabijin na Channels, ranar Alhamis inda ya ce ba zai yi wa gwamnan katsalandan ba a harkokin mulkinsa.

A cewarsa, ba zai tilasta wa gwamnan waɗanda ya ke so a ba muƙaman ba duk da zargin alaƙanta shi da rikicin siyasar da ya jefa jihar a dokar ta-ɓaci.

Ya ce, koda ace gwamnan zai nemi shawararsa, zai shawarce shi ne da ya yi mulkinsa kai-tsaye ba tare da dogaro da wani ba.

Tsohon gwamnan na Ribas ya kuma ce burinsa shi ne Fubara ya ɗora daga inda ya tsaya wajen yi wa al’umma hidima ta yadda za a ciyar da jihar gaba a fannoni masu yawa.

Ya ƙara da cewa, ya san ya bar jihar a mataki na ci-gaba ta yadda za ta iya gogayya da Jihar Legas wajen samun ababen more rayuwa.

By Babaji