Kano: Za a dasa bishiyoyi 10,000 a Ƙaramar Hukumar Bichi

Spread the love

Tuwassan bishiyoyi 10,000 aka samar domin dasawa a Karamar Hukumar Bichi a wani mataki na yaƙi da kwararowar hamada a faɗin karamar hukumar.

Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ya faɗa haka a wajen ƙaddamar da dashen bishiyoyin tare da raba tuwassan itatuwan ga dagatai da masu unguwanni dake Karamar Hukumar Bichi.

Hamza Sule Mai Fata, wanda ya samu wakilcin Daraktan Mulki na ƙaramar hukumar, Alhaji Abba Muhammad Diso, ya bayyana cewar waɗannan tuwassan bishiyoyi guda 10,000 Gwamnatin jihar Kano ce ta samar da su, kamar yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarni a samar da su a dukkanin ƙananan hukumomi 44 da ke jihar.

Ya kuma bayyana cewa dashen bishiyoyin a karamar hukumar, wani mataki ne da zai kara taimakawa wajen yaki da kwararowar hamada, musamman ma ganin yadda ƙaramar hukumar take maƙwabtaka da wasu ɓangarorin ƙasar nan da ma jamhuriyar Nijar.

“Dangane da abubuwan da suke faruwa yanzu a duniya na canjin yanayi na zafi da sauransu da yadda Karamar Hukumar Bichi take kusa da Nijar, bisa wannan matsala ta hamada mai girma Gwamna ya sahale mana tushe 10,000 domin a dasa su a ciki da wajen wannan karamar hukuma. Dangane da kula da su kuma mai girma shugaban Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya ce, duk wanda aka ba in sha Allahu za a ba shi kwandon da zai ci gaba da kula da ita har ta rayu.” In ji shi.

Daga nan kuma ya buƙaci dagatai da masu unguwannin da kuma sauran al’uma da su sanya idanu sosai wajen renon wadannan bishiyoyi da za su dasa a yankunan nasu.

A nasa jawabin, shugaban Sashen Gona da Albarkar Kasa na Karamar Hukumar Bichi, Malam Rabi’u Haruna, ya yi bayani mai tsawo dangane da mahimmancin dashen itatuwa.

“Hakika bunkasa dashen itatuwa ba karamin aikin alheri ba ne domin yana cikin sadaqatul jariya, kuma zai samar da kyakkyawan yanayi tare da sanyaya muhallinmu, sannan zai kare muhallinmu daga barazana ta iska, sanan zai kare kasa daga zaizaya da ainahin hamada kuma za a rika amfani da wadannan itatuwa ta fannin magunguna, saboda haka wannan ba karamin al’amari ba ne.” In ji shi.

A lokacin taron dai, Hakimin Bichi Galadiman Kano, Alhaji Mannir Sanusi, shi ne ya kaddamar da raba tuwassan bishiyoyin ga wasu daga cikin dagatai dake karamar hukumar, a wani mataki na kaddamar da shirin. Kuma taron ya samu halartar dukkanin dagatai 44 dake Karamar Hukumar Bichin da shugabannin sassa da kansiloli da sauran masu ruwa da tsaki a kan harkokin ayyukan noma da gudanar da al’amuran Karamar Hukumar Bichi, kamar yadda Jamila Abdullahi R/Lemo,wato jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar ta ruwaito.

By Babaji