
An yi kira ga ɗaukacin al’ummar ƙananan hukumomin Jihar Kano da su yi koyi da Ƙaramar Hukumar Bichi wajen saka kishin yankinsu ba tare da bambancin siyasa ba.
Shugaban kasuwar zamani ta Bichi, Alhaji Garba Tukur ne ya bayyana haka yayin tattaunawarsa da jami’ar yada labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo.
Alhaji Garba Tukur ya ce, kishin juna da haɗin kai na al’ummar Bichi ya kawo ci-gaba da bunƙasar karamar hukumar duba da ayyukan gani da ido da bambanci na siyasa bai hana ta rabauta da su ba waɗanda suka hada da; gina babbar kasuwa da samar da wutar sola a lungu da sako da intalok da titunan kwalta da gine-ginen wasu ɓangarori a babban asibitinsu irin na asibitin koyarwa, da samar da magani tare da ɗaga matakin asiitin zuwa gaba.
Sannan, kowace mazaɓa an yi hanyoyi da manyan gadaje a titunan ƙauyuka da bada taki ga manoma.
Ya ƙara da cewa, wannan nasara ta samu ne sakamakon ilimi da wayewa tare da zumunci da jami’ar yankin suka sa a gaba.
“Al’umma ce a gabansu, Cigaban al’umma ne a gabansu, garin ne a gabansu, sannan filin da ake yin aikin nan na gwamnatin jiha ne, kuma ita ce ta ba shi, saboda haka ba maganar siyasa ake yi ba, maganar cigaba zalla ake yi”, inji shi.
Daga bisani na gana da shugaban kungiyar kasuwar ta zamani, Alhaji Abubakar Muzahim, inda shi ma ya jaddada cewa.
“Mu kwankwasiyya ce ta kawo mu, ciyaman din Karamar Hukumar ne ya kawo mu, shi kuma GM Dan Majalisar Tarayya ne ya bayar da shi, amma muna yin aiki tare a matsayin uwa daya uba daya, ba tare da nuna bambanci na siyasa ba.”
Haka kuma, ta tattauna da wasu daga cikin ‘yan kasuwar domin jin ta bakinsu.
- “Da damina wajen nan baya zaunuwa, da ikon Allah kuma da ya zo ya duba yaga ya dace ya yi temfirari, kuma ya yi, daga nan har zuwa bakin titi duk aikin shugaban Karamar Hukumar Bichi ne”, inji Sani Isyaku Abubakar.
- “Allah ya kawo shugaban karamar hukuma mai tausayi, ya kira mu, ya yi mana rumfuna ya saka mu
Ba,tare da ya ce sai mun biya shi wasu kudi ba, gaskiya ya kawo mana cigaba a Karamar Hukumar Bichi, ba daya ba ba biyu ba, cigaba iri-iri sosai” – Isah Danbaba mai kayan miya. - “Wanda Allah ya ciyar ya rabauta da wannan, ya zo dnn abin da Allah ya hore masa ya sa ya kama sana’a”, inji Malam Sabitu Mai Kifi.
A yayin da yake jawabinsa, Janar Manaja na kasuwar, ya tunasar da al’umar Karamar Hukumar Bichi, da su ci gaba da kula da alkinta abubuwan alherin da karamar hukumar ta samu tagomashi kamar yadda suka saba, inda a karshe, ya ja hankalin al’uma da su yi koyi da karamar hukumar, ta hanyar kallonta a matsayin littafin da za a karanta domin samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.







