
KƘaramar ukumar Bichi ta yi jan hankali ga iyaye da sauran al’ummar yankin da su riƙa kai ƴaƴansu riga-kafi da kuma gaggauta kai su asibiti idan cutar mashako ta kama su.
Shagaban Shashen Lafiya a yankin, Kabiru Abubakar Gwarzo ne ya yi jan hankalin a lokacin da yake ƙarin haske kan iftila’in cutar da ta ɓullar a wasu yankunan jahar ciki har da Ƙaramar Hukumar ta Bichi.
Abubakar Gwarzo, ya bayyana cewa da samun rahoton cutar ta ɓulla a wani sashi na Karamar Hukumar ta Bichi, ba tare da bata lokaci ba, aka tura jami’an lafiya yankin da abin ya faru, inda aka yi musu allurai da duk abin da ya kamata.
Ya kuma buƙaci al’ummar yankin da su bai wa jami’an lafiya haɗin kai domin samun nasarar kawar da cutar.
“Wannan larura da aka samu daga yankunanmu, jan hankali da za yi a kai shi ne; magidanta da iyayen yara a rika kawo yara asibiti rigakafi na allurori da ake yi, dimin hakan shi ne zai kare mana yaranmu daga kamuwa da wata cuta.”
Ya ƙara da cewa, shugaban Karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ya duƙufa wajen samar da dukkanin abubuwan da ake buƙata, wajen bunƙasa ƙoshin lafiyar al’umar yankin.
Wasu daga cikin Iyayen yaran da suka rasu sanadiyyar iftila’in, sun bayyana yadda lamarin ya faru ga ƴaƴansu.
“Lokaci daya suka fara kamuwa da cutar ta mashako, aka kai su asibiti gaba daya. Da farko Hassan ne ya fara rasuwa, sannan ta biyu Firdausi, sannan ta uku Usaina, na hudu kuma shi ne Usaini, na biyar din wanda aka yi, yau kwana uku ke nan, shi ne Hassan”, – Malam Habibu Da’u kakan yaran.
Waɗanda suka je ta’aziyya gidan yaran da suka rasun, a madadin Majalisar Karamar Hukumar ta Bichi, sun haɗa da; Sakataren Mulki da shugabannin sashe da kansiloli da dai sauransu, kamar yadda Jamila Abdullahi R/Lemo, wato jami’ar yaɗa labaran Bichi ta ruwaito.





