
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mutane biyu sun rasa rayukansu a lokacin da wani abin fashewa ya tarwatse a masana’antar makaman sojoji (DICON) da ke yankin Kakuri a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu, Jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa, an jiyo ƙarar tashin dom ɗin a da dama daga unguwannin birnin ciki har da Chikun da Kaduna ta Kudu a safiyar yau Asabar.
Haka kuma jama’a da dama sun jikkata yayin faruwar al’amarin, wanda kawo yanzu ba a san musabbabinsa ba.
Tuni aka garzaya da waɗanda suka raunata zuwa asibitoci mafi kusa da wajen da abin ya faru.
A yayin da aka gudanar da bincike a kai ne za a samu ƙarin bayani game da abinda ya sabbaba da kuma matakin damejin da ya yi.
Al’amarin ya jefa tsoro acikin al’umma musamman ganin yadda DICON ke da matakan tsaro masu ƙarfi da kuma kusancinsa ga wasu yankunan birnin.
A shekarar 1964 aka samar da masana’antar domin ƙera makamai, alburusai, ababen fashewa da wasu kayan yaƙi ga sojojin Nijeriya.
