Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Katsina ta amince da naɗa Dakta Basira Umar a matsayin babbar magatakardar babbar Kotun Jihar Katsina, (Chief Registrar Of Katsina State High Court),
Wannan shine karo na farko da aka naɗa mace a wannan matsayi tun da aka ƙirƙiro Jihar Katsina a shekarar 1987.
A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na babban kotun Musa Usman,ya ce kafin naɗa Dakta Basira a wannan matsayi,itace daraktan kula da kotunan sasanci a jihar.
Ta sami wannan muƙami ne bayan da tsohon babban magatakardar babban kotun Mustapha Hassan Ruma ya yi ritaya.
