Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Wani labari da ya mamaye kafafen sadarwa a cikin wannan mako mai ƙarewa shi ne na batun sulhu da aka yi da wani gungun wasu ’yan bindiga a ƙaramar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina ƙaraashin jagorancin babban ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Ado Alero.
Wannan na zuwa ne sakamakon yadda rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a jihohin Katsina, Zamfara, Sakkwato, da wasu sassan jihohin Kebbi, Naija, Filato, Binuwai, da Taraba. Wannan ya haɗa shiyyoyin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya. Rayuka da dama sun salwanta sakamakon hare-haren ’yan bindiga kan jama’ar ƙauyuka da birane a waɗannan jihohi. Bayan asarar rayuka da dukiyoyi, ga batun cin zarafin ɗan adam da garkuwa da mutane, wanda ya zama ruwan dare, kuma babbar hanyar samun kuɗaɗen sayen manyan makamai.
Wani rahoto da jaridar Blueprint Manhaja ta fitar a makon da ya gabata ya bayyana cewa, Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa an samu raguwar ayyukan ta’addanci da kaso 70 a faɗin jihar, biyo bayan ɗaukar muhimman matakai wajen kawo ƙarshen matsalar tsaron da ke addabar sassan ta.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Dr. Nasir Mu’azu ne ya bayyana haka yayin wani muhimmin taron bayar da rahoton halin da ake ciki kan tsaro, wanda Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya shirya.
Cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta fitar, ta bayyana cewa irin matakan da gwamnatin ke ɗauka ya sanya da yawa daga cikin jagororin ‘yan bindiga ajiye makamansu tare da neman a yi sulhu.
Sanarwar ta kuma ce jagororin al’umma na ci gaba da yunƙurin ɗaukar matakan yin sulhu da ’yan bindiga a wasu ƙarin yankunan jihar. Babu mamaki ganin abubuwan da suka faru na sulhu da ’yan bindiga a ƙaramar Hukumar Faskari.
Abu ne mai ban tsoro da takaici ganin yadda waɗannan ‘yan ta’adda ke fitowa da makamai iri-iri da baburansu cikin izza da gadara suna ratsa jama’ar da suke cutarwa, da sunan an zo sulhu. Kuma a maimakon a ajiye makaman sai ma suka zama kamar wani abin ado, ana taƙama da nuna isa. Har da faɗar maganganu na rashin tsoro na rashin nadama kan abubuwan da suka yi.
Kodayake ba mu san ko nan gaba gwamnati za ta shirya taron ajiye makamai da yin afuwa ba, amma dai gaskiya dole a sake duba lamarin nan. Duk da cewa muna goyon bayan sulhu da samar da ingantaccen zaman lafiya da tsaro, amma kada hakan ya nuna gazawa ko ƙasƙanci ga jami’an tsaron mu na gwamnati da hukumomin da ke sa ido kan harkokin siyasa da tsaro.
Muna yabawa ƙwarai da rawar ganin da jami’an tsaron mu ke takawa wajen shawo kan waɗannan matsaloli, wanda daga cikin tasirin matakan da suke ɗauka ne har ta kai ga su ’yan bindigar da kansu suka fito neman sulhu. Kodayake kamar yadda masu nazarin al’amura ke bayyanawa, akwai buƙatar jama’a da jami’an tsaro su ƙara hattara kuma su zama cikin kula, domin ta iya yiwuwa wannan ya bai wa sauran ’yan ta’addan da ba su shiga cikin tsarin sulhu ba su samu damar sake shiga cikin jama’a suna sake nazartar abubuwan da za su sake shigowa daga baya su cutar da jama’a.
Sannan an lura, matakan da jami’an tsaro da masu taimaka musu ke ɗauka ya sa sun kasa sakewa tare da takurewa a cikin daji, duk da yake suna samun wakilansu a cikin jama’a da ke yi musu fasaƙaurin duk abubuwan da suke buƙata. Sai dai hakan ba ya wadatar da su, saboda rashin samun yadda za su kashe kuɗaɗen da suke tarawa, daga ta’addancin da suke yi. Suna buƙatar sakewa da walwala, don su mori abin da suke samu. Kuma matan su suma su yi walwalarsu a cikin jama’a.
Babu shakka sulhu alheri ne, ba ga jama’ar gari kaɗai ba, har ma da su ’yan bindigar. Kuma zai bai wa kowanne ɓangare damar samun natsuwa, ya tunkari wasu abubuwa da za su kawo wa rayuwar sa cigaba. Kamar yadda aka amince za a ƙyale ’yan bindiga shiga gari su yi cuɗanya da kasuwanci da jama’a, ba tare da suna yawo da ado da makamai a kafaɗunsu ba. Sannan kuma su ma jama’ar gari za su samu damar zuwa gonakinsu su yi noma don su samu abincin da za su ciyar da iyalan su da kuma su sayar. Sannan a wasu wuraren na ji cewa, daga ɓangaren ’yan bindigar suna zama garkuwa ko masu tsaron al’ummar da suka yi sulhu da su, domin kare su daga wasu ’yan ta’addan da ka iya kai musu hari.
Mai yiwuwa wannan na daga cikin fa’idojin da gwamnati ke cewa ana samu, sakamakon sulhun da ake ƙullawa. Amma wani muhimmin jigo da ya kamata mu duba harwayau shi ne, batun kare haƙaokin ɗan’adam, sakamakon ƙorafin da wasu shugabannin ’yan bindigar ke yi na zalunci da kisan gillar da ake musu da jama’ar su, wanda hakan ke sa su yin ramuwar gayya. Kamar yadda aka sani, lallai a kowacce al’umma ana samun ɓatagari, amma hakan bai sa laifin wani ya shafi wani ba. Bibiyar duk wani bafulatani ko duk wata ruga ana kashewa, don ana zargin wani daga ɓangaren su ya aikata laifi, ba daidai ba ne. Hakan ne ke ƙara ta’azzara taɓarɓarewar tsaro, a kasa shawo kan yawan kai hare-hare.
Lallai mu sani su ma Fulani, mutane ne kuma ’yan ƙasa, suna da damar rayuwa da shiga ko’ina su yi mu’amalarsu ba tare da an tsangwame su ko an cutar da su ba. Matuƙar su ma za su yi rayuwar su ba tare da sun shiga haƙƙin kowa ba. Yi wa kowanne ɓangare adalci da mutunta haƙƙoƙin juna ne kaɗai zai sa sulhun da ake yi ya haifar da ɗa mai ido, a cimma nasarorin da ake buƙata.
Hausawa da Fulani abokan zama ne tun kafin jihadin Shaihu Usmanu, kuma cuɗanya da auratayya ta sa an zama ɗaya. Yaƙi da juna da kashe-kashe don neman durƙusar da kowanne ɓangare ba abu ne mai kyau a garemu ba. Lallai mu tuna kuma mu kiyaye da dokokin kiyaye haƙƙoƙin ɗan’adam na Majalisar ɗinkin Duniya, da kundin tsarin mulkin ƙasa, da suka bai wa kowanne mutum ’yancin yin rayuwa kamar kowa, ba tare da nuna ƙasƙanci ko ƙyama ba.
Fulani ma kamar sauran ƙabilu, mutane ne kuma ’yantattu, da babu wanda doka ta bai wa damar cutar da su ba tare da sun aikata laifin komai ba. Ƙyamar da ake nuna musu na daga cikin abubuwan da suke ƙara tunzura wasun su har suke aikata abubuwa marasa kyau. Su ma kuma su sani kamar yadda suke so a gansu da daraja da mutunci, lallai su yarda kowanne ɗan adam, Bahaushe da duk wata ƙabila, mutane ne masu daraja da ’yanci, wanda bai dace a yi garkuwa da su ko a bautar da su, ko a kwashe musu dukiya ko a yi fasiƙanci da iyalinsu ba. Kamar yadda masana harkar zaman lafiya ke cewa, zaman lafiyarka na da alaƙa ne da zaman lafiyar maƙwafcinka.
Babu wata al’umma da za ta yi rayuwa ita kaɗai ba tare da cuɗanya da wata ƙabila ba, matuƙar za a zauna tare cikin girmamawa da mutunta bambance-bambancen juna. Lallai Hukumar da ke Kula da Yaɗuwar ƙananan Makamai ta ƙasa ta ƙara tashi tsaye da ganin ta haɗa kai da sauran jami’an tsaro, wajen yaƙi da yaɗuwar makamai a hannun mutanen da ba hukuma ba. Hakan zai taimaka wajen rage aikata laifuka da ayyukan ta’addanci a cikin ƙasa.
