Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A ƙoƙarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa, a Jihar Katsina, ƙananan hukumomin Sabuwa, Ɗandume da Faskari sunyi zaman sasanci da yan bindiga na yankin.
Shugabannin ƙananan hukumomin Sabuwa, Ɗandume da Faskari
su ka jagoranci sasanci da ‘yan bindigan da ke da sansani a garuruwan Kabalawa Dugun Ma’azu dake cikin ƙaramar hukumar Sabuwa.
Daga ɓangaren ƴan bindigar da su ka jagoranci sasancin, akwai Kabiru, Kachalla Rusku, Kachalla Murtala, Kachalla Mai saje, Kachalla Dawa da dai sauran su.
Shugabannin ƴan bindigar na bayyana jin daɗin su akan sasanci tare da yaba ma shugabannin ƙananan hukumomin akan dattako da suka nuna gami da son zaman lafiya da suke nemar wa al’ummar su.
Shugabannin yan bindigan, wanɗada suka hada da Ardo Abdulsalam Fatika, Idi Muwange, Kachalla Dawa, Alh. Labi da Kachalla Rusku sun tabbatar ma tawagar ta al’ummar ƙananan hukumomin sun bayar da amincewa da zaman lafiya tare da daina kai hare, hare da satar mutane a faɗin ƙananan hukumomin.
A nasu jawabin shugabannin ƙananan hukumomin Sabuwa da Ɗandume Hon. Sagir Tanimu da Hon. Bishir Sha’aibu sun nuna jin daɗin su da gamsuwarsu akan tsarin yarjejeniyar da aka kulla tsakani.
Sun kuma bada tabbacin da cewa zasu cika alƙawuran da suka ɗauka, na samar da ababen more rayuwa ga al’ummar fulanin, wanda yafi ƙarfin su kuma, za su kai zuwa ga ma gwamnatin jihar domin ɗaukan mataki.
Da yake jawabi, shugaban kwamitin sasanci Dr. Salisu Lada ya bayyana dokokin yin sulhu guda 17, biyar da gwamnati ta gindiya ga al’ummar da suka amince da yadda da ayi Sulhu.
Shima a nashi jawabin, wakilin Sarkin kogon Katsina Hakimin Sabuwa, wanda ya samu wakilcin Yarima Alhaji Ibrahim Bello kogo ya nuna jin daɗin shi, akan wannan yarjejeniyar zaman lafiya da akayi a yankin ƙaramar hukumar Sabuwa da sauran ƙananan hukumomin.
Yarima kogo ya cigaba da bayyana yadda dangantaka ta zumunci dake tsakanin Fulani da Hausawa a da, amma wasu dalilai su ka gitta su ka ɓata wannan dangantaka.
Ya yi fatan dawo da wannan dangantaka, zumunci da ƙaunar juna kamar yadda take a tsakanin Fulani da Hausawa.
Wakilan hakimin ya yi addu’a Allah ya ƙara zaunar da al’umma lafiya tare da samun arziki mai ɗorewa.
Taron ya samu halartar ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Sabuwa Hon. Ibrahim Danjuma, Mai baiwa Gwamnan jihar Katsina shawara akan makarantu lafiya Hon. Mammada, Tsoho Shugaban ƙaramar hukumar Sabuwa Hon. Faruk Hayatu.
Sauran sun haɗa da Hon. Ya’u Nowa, Masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomin, uwayen ƙasa da sauran al’ummar gari maza da mata da sauran su.
Ya zuwa yanzu ƙananan hukumomi kusan 10 ne suka rungumi zaman sasanci da ƴan bindiga a yankunan su.
