Ƙaramar hukumar Matazu ta yi sulhu da ‘yan bindiga na yankin a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙaramar hukumar Matazu Hon. Shamsuddeen Muhammed Sayaya da kachalla Muhammadu na ɓangaren ‘yan bindiga ne suka jagoranci zaman sulhun a madadin ɓangarorin mutanen su a wajan taron.

Kacallah Muhammadu yana ɗaya daga cikin shugabannin ‘yan bindigan da su ka addabi yankin ƙaramar hukumar Matazu da wani yanki na ƙaramar hukumar Ɗanmusa.

A jawabin sa wajen taron, Fagacin Katsina kuma Hakimin Matazu Alhaji Iro Maikano ya nuna jin daɗin sa a kan wannan sulhu da a kayi tare da yan uwa Fulani, da kuma yin kira a garesu da a yafe ma juna a haɗu a zauna lafiya.

Shima a nashi jawabin, shugaban yan bindiga a Yankin Kacallah Muhammadu ya bayyana cewa “Ni tare da mabiyan na mun amince da wannan sulhu domin a zauna lafiya,”inji Kachalla.

Ya bada tabbacin cewa sun yi alƙawarin daina kai hare, hare da satar mutane a ƙaramar hukumar Matazu, sannan kuma za su sako dukkan mutanen dake tsare a hannunsu da sukayi garkuwa dasu.

Sauran waɗanda su ka tofa albarkacin bakinsu daga cikin Fulanin dajin, sun haɗa da Mannore, Sani Yellow, sun bayyana ƙorafe, ƙorafen su akan jami’an tsaro tare da yin kira da a ɗauki mataki hana jami’an tsaro su takura masu, domin ɗorewar zaman lafiyar da aka samu.

A nashi jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Hon. Shamsuddeen Muhammed Sayaya ya nuna farin cikinsa akan nasarar da aka samu ta sulhu da fulanin daji domin samun zaman lafiya a ƙaramar hukumar Matazu.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ɗauki lokaci mai tsawo yana gabatar da jawabinsa mai matukar mahimmanci, inda daga ƙarshe, a madadin al’ummar ƙaramar hukumar ya yi kira da a kafa wani kwamiti da zai sa ido wajen yadda ake aiwatar da yarjejeniyar.

By ukarofi