Daga SHEHU MUSTAPHA CHAJI
Kasancewar Jihar Kano cibiyar kasuwanci da dimokuraɗiyya a Arewacin Najeriya na daga cikin dalilan daya sa shugaban ƙasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu ke cigaba da bai wa jihar kulawa ta musamman. Cikin ayyukan cigaban ƙasa da Shugaba Tinubu ya sahale a yiwa Jihar Kano a wannan makon sun haɗa da ware Naira Biliyan 12 dan samar da wutar solar a Asibitin Malam Aminu Kano da zai samar da megawatt bakwai da hakan zai sanya asibitin sauka daga layin lantarki ta ƙasa.
Ana kuma cigaba da aikin gina bene mai hawa biyar na sashin bayar da kulawar gaggawa (Emergency) a asibitin. A wannan shekarar kawai Shugaba Tinubu ya sahale a kashe Naira Biliyan 26 a asibitin Malam Aminu Kano domin mayar da asibitin sahun manyan asibitoci a Afrika.
Ƙarin cibiyoyin da suka amfana da ayyukan cigaban ƙasa a Jihar Kano a wannan makon suna haɗa da:
Jami’ar Bayero da za’a sanya wutar solar megawatt biyar zuwa shida.
Jami’ar Aliko Ɗangote dake Wudil da za’a sanya wutar solar megawatt huɗu.
Asibitin Murtala da za’a sanya wutar solar megawatt uku
Asibitin Nasarawa da za a sanya wutar solar megawatt uku.
Samar da wutar solar ga waɗannan cibiyoyi zai rage musu yawan kuɗaɗen da suke kashewa kan lantarki da dizel da kula da janeretoci da sauransu.
Wasu yan adawa a kullum suna ƙoƙarin yaɗa farfagandar cewa babu abinda Shugaba Tinubu yayiwa Jihar Kano na cigaba. Zancen gaskiya akwai ayyukan cigaban Ƙasa da dama da aka fara ko aka cigaba da aikin su ƙarkashin mulkin Shugaba Tinubu. Kaɗan daga cikin su sun haɗa da:
1) Cigaba da aikin gina layin dogo daga Kano zuwa Kaduna.
2) Cigaba da aikin gina dubban gidaje masu sauƙi a wasu ƙananan Hukumomin Jihar Kano.
3) Ayyukan gyara da maida filin jirgin sama na Malam Aminu Kano kamar na ƙasashen da suka cigaba a duniya.
4) Cigaba da aikin tagwayen titi daga Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja.
5) Cigaba da aikin titin Bypass a gabashin Kano.
6) Cigaba da aikin tagwayen titi daga Kano zuwa Katsina.
7) Cigaba da aikin titin Kano zuwa Hadejia.
8) Cigaba da aikin bututun gas (AKK)
9) Aikin jirgin ƙasa na zamani da zai ratsa birnin Kano.
10) Cigaba da aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Dutse zuwa Maradi.
11) Kulawa ta musamman kan tsayar da zaizayan ƙasa a ƙananan hukumomi 16 a Jihar Kano.
12) Aikin gina sabbin mugudanan ruwa daga Dam ɗin Tiga da Dam ɗin Karaye da Dam ɗin Kafin Chiri zuwa Kano ta Kudu dan bunƙasa noman rani.
13) Cigaba da aikin tagwayen titi daga Kano zuwa Maiduguri.
14) Cigaba da aikin titin Bypass mai tsawon kilomita 38 a Arewacin Kano.
15) Gyara da ƙara girman Dam ɗin Tiga.
16) Ɗaga matsayin makarantar gaba da sakandare dake Kabo zuwa jami’ar kimiya da fasaha.
17) Sahalewa a gina makarantar gaba da sakandare a Rano.
18) Gyara dama damai 16 a Jihar Kano.
19) Aikin gina cibiyar taron ƙasa da ƙasa a ƴar Gaya.
Saboda taƙaita bayanai kan ayyukan cigaban ƙasa da Shugaba Tinubu ke yi a Jihar Kano zamu tsaya a haka.
Kanawa suna ta godiya da jinjina ga Shugaba Tinubu kan yanda yake ta kwararo ayyukan cigaban ƙasa a Jihar Kano. Tunda aka dawo mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999 Jihar Kano a karon farko ta san ana mulkin dimokuraɗiyya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kwantar da hankalin sa kan batun zaɓen shekarar 2027 domin zasu bashi ƙuri’u kusan miliyan biyu.
