Kakakin Majalisar Katsina zai ɗauki nauyi mata ‘yan hisbah karatun kiwon lafiya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kakakin Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina, Rt. Hon Nasir Yahaya Daura, ya ɗauki nauyin karatun Mata yan hisbah guda 10 kan kiwon lafiya, domin su kula da Mata yan uwansu, ƙarƙashin hukumar hisbah da ke Daura.

Haka kuma ya ɗauki nauyin karatun yara marayu guda 20, wanda za su yi karatu a makarantar ‘yan sanda da ke Daura (Police Children School).

Kakakin Majalissar yayi wannan bayanin ne a lokacin da ya halarci taron yaye sabbin jami’an hisbah 200, a babban masallacin Juma’a dake low-cost Daura, bayan kammala samun horo na tsawon wata shidda, a hannun ƙwararrun jami’an hukumar.

Rt. Hon. Nasir Yahaya ya sanar da hukumar cewa, Gwamnatin Jihar Katsina za ta cigaba da goyawa hukumar hisbah baya, da bata duk wani cikakken goyan bayan da hukumar ke buƙata, domin ta cigaba da gudanar da ayyukanta na alkhairi, gyaran tarbiyyar al’umma, da kuma faɗa da abubuwan alfasha.

“kwanan nan Majalissar Dokoki ta yiwa Dokar da ta ƙirƙiri hukumar hisbah garambawul, inda ta ƙarawa hukumar ƙarfi, domin ta cigaba da gudanar da ayyukan ta na alkhairi a Jihar Katsina,”inji kakakin majalisar.

A cewar sa hakan ƙarara ya nuna cewa Gwamnatin Jihar Katsina tana goyan bayan hukumar. Sanan mai girma kakaki daga yau shima ya zama mamba na hukumar hisbah a ƙaramar hukumar Daura, inda ya amshi form ɗin sa a hannun shugabanta na Daura.

Kakakin Majalisar ya roƙi hukumar ta hisbah, da ta sanya a cigaba da yiwa Jihar Katsina addu’a, akan Allah ya kawo zaman lafiya mai ɗorewa da yaɗuwar arziƙi a Jihar Katsina.

By ukarofi