
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya koka game da kisan Somtochukwu Christelle Maduagwu, wadda ƴar jarida ce a gidan talabijin na Arise, a yayin wani fashi da ɓarayi suka ƙaddamar a gidanta da ke Katampe a Abuja a daren ranar Lahadi wayewar Litinin.
A wata takarda daga Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu ya bayyana ƴar jaridar a matsayin ƙwararriya a fannin aikinta wadda ta rayu na gajeren zango bisa iftila’in da ya same ta.
Don haka ya umarci hukumomin tsaro da su ƙaddamar da bincike akan kisan nata, yana mai alwashin sai an hukunta dukkan wanda aka samu da hannu a ciki.
Ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalanta, abokan aikinta da ɗaukacin fagen aikin jarida, yana mai jaddada aniyar gwamnatinsa ta cigaba da bai wa ƴan ƙasa kariya da yaƙi da manyan laifuka masu cutar da al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa, gwamnatin nasa za ta ruɓanya ƙoƙarinta wajen tabbatar da bin doka da oda da bada kariya ga sake samun faruwar irin haka a nan gaba.
