
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Ahmed Mohammed, da aka fi sani da Barista Ahmed Lauya, wanda kuma shi ne kwamishinan zaɓe na hukumar zaɓe ta jihar Neja da direbansa da tsohon Shugaban SUBEB Mohammed Bawa Niworu da kuma wasu matafiya ta dama.
Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya auku ne a safiyar ranar Litinin, 29 ga watan Satumba a titin Zugurma zuwa Ibbi zuwa New Bussa kusa da filin shaƙatawa na ƙasa da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu.
Wata majiya ta ce al’amarin ya faru ne a lokacin da mutanen ke kan hanyarsu ta dowawa daga Borgu, inda aka ga motarsu a fake a gefen titi tare da wayoyinsu aciki.
An gano cewa ƴan bindigar sun tare hanyar ne a wani waje dake gaba da shingen bincike na ƴan sanda kafin afka wa matafiyan.
Ana haka ne ƴan sanda suka kai ɗauki inda suka yi ba-takashi da su, lamarin da ya yi sanadin raunata jami’i ɗaya da garzayawa da shi zuwa wani asibiti.
Wani diraban motar kasuwa da ya tsere wa lamarin ya ce aƙalla motocin Sharon uku maƙare da fasinjoji ne ƴan bindigar suka tafi da su daji.
Da yake tabbatar da batun, Kakakin ƴan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya ce wata motar ƴan sanda ta samu harbe-harben bindiga a yayin arangamar.
Ya kuma ce, hukumomin tsaro suna gudanar da bincike akan al’amarin tare da ƙoƙarin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
