
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani abin alhini ya jefa al’umma cikin jimami a Ƙaramar Hukumar Ibaji da ke Jihar Kogi bayan wani hatsarin kwale-kwale a jiya Talata ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 20 a Kogin Neja.
Rahotanni sun bayyana cewa, kwale-kwalen, wanda ya jigata, ya taso ne daga yankin Onugwa na ƙaramar hukumar inda ya nufi babbar kasuwar Ilushi da ke jihar Edo, inda ya kife a wani yanki da ke tsakanin ƙauyukan Okpu da Odumomo.
Shaidu sun ce kwale-kwale ya ɗebo mutane sama da kima waɗanda galibinsu mata ne da ƙananan yara da ke shirye-shiryen bikin ranar ƴancin kai.
Tuni wasu ƴan sa kai suka garzaya wajen domin ceto su, inda suka ciro gawarwaki guda 20 daga cikin kogin yayin da ake cigaba da neman sauran. An kuma ceto was shida a raye.
Rundunar ƴan sandan jihar ta bakin Kakakinta, SP William Aya, ta tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce jami’ai suna ƙoƙarin gano a wani ɓangare na kogin iftila’in ya faru a tsakanin yankunan jihohin Kogi da Edo.
