Nijeriya ta yi asarar biliyan N52.26 sakamakon ’yan damfara a 2024 – FCDO

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Bayanai daga Hukumar ’Yan Sanda ta ƙasa da ƙasa (Interpol) sun nuna cewa ayyukan zamba da damfara a Afirka sun ƙaru da kashi 3,000 a cikin 2024.

Shugaban Hukumar Kula da Ci Gaban ƙasashe Rainon Afrika (FCDO) Sorrel Eɓans, wanda ya bayyana hakan a wajen ƙaddamar da Tsarin Daƙile Zamba na ISO37003:25 a ranar Talata a Abuja, ya ƙara da cewa Nijeriya ta yi asarar Naira Biliyan 52.26 sakamakon zamba a shekarar 2024.

Adadin, a cewar Eɓans, yana nuna ƙaruwar kashi 295 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

“A cikin yanayin da Nijeriya ta yi asarar biliyan 52.26 ta hanyar zamba a shekarar 2024, Wataƙila ma adadin ya ƙaru. Wannan adadi na Naira Biliyan 52.26 ya nuna ƙaruwar kashi 295% a shekarar da ta gabata,” inji Eɓans.

ƙungiyar Standard Organisation of Nigeria tare da haɗin gwiwar British Standards Institution (BSI) ne suka shirya taron.

Jami’in na FCDO ya bayyana cewa a cikin 2024, zambar da aka samu ya ƙaru da kashi 167 cikin 100, wanda ke yin barazana ga asalin kamfanoni da kuma lalata harkokin kasuwanci.

Wani rahoto na zamba na duniya ya nuna cewa, yankin kudu da hamadar sahara ne ke da matsalar zamba ta kasuwanci a duniya, inda kashi 34 cikin 100 na dukkan harkokin kasuwanci a nahiyar ke da kashi 25 cikin 100 a duniya.

A jawabinsa na maraba, Babban Darakta na Hukumar Standard ta Nijeriya (SON), Dokta Ifeanyi Chukwunonso Okeke, ya ce zamba har yanzu yana kawo cikas ga ci gaban ƙasa.

A cewarsa, zamba yana zubar da amana, ciki har da tsadar harkokin kasuwanci, yana hana saka hannun jari na ƙasashen waje tare da hana ‘yan ƙasa albarkatun da ake buƙata domin samar da ababen more rayuwa da zamantakewa. 

Daraktan ya yi bayanin cewa tare da ISO 37003-2025, “yanzu mun rungumi ingantaccen tsari don rigakafin zamba, ganowa da daƙilewa.”

Ya ce, ƙa’idar ta samar da tsarin da aka sani a duniya don hana ayyukan damfara kafin su faru, gano zamba yadda ya kamata idan ya taso da kuma mayar da martani mai tsauri don tabbatar da rage ɓarnar.

Haka kuma, Ministar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, ta bayyana damuwarta cewa zamba na daƙile ci gaban tattalin arzikinmu.

Ministar wadda ta samu wakilcin Daraktar Reform Dr. Jachyma Agu, ta ce yana ƙara tsadar kasuwanci, yana zubar da kwarin gwiwar masu zuba jari, da daƙile ayyukan ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma lalata tattalin arziki.

By ukarofi