
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Bola Tinubu ya amince da saukar Farfesa Mahmood Yakubu daga muƙamin Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC) bayan ƙarewar wa’adinsa na biyu kuma na ƙarshe.
Sakamakon girmamawa da hidimar da ya ba wa ƙasa a muƙamin, Shugaba Tinubu ya ba shi kyautar girmamawa ta ƙasa ta “Commander of the Order of the Niger’ (CON).
Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.
A tsawon shekaru goma da ya jagoranci hukumar, Farfesa Yakubu ya jagoranci lamuran manyan zaɓukan 2019 da na 2023, da gabatar da sababbin fasahohi kamar su INEC Result Viewing Portal (IReV) don inganta gaskiya da wajen fitar da sakamako.
A wata takarda da ke ɗauke da 3 ga watan Oktoba, 2025, Farfesa Yakubu ya miƙa godiyarsa ga Shugaba Tinubu akan damar da aka ba shi na shugabantar hukumar har wa’adin biyu.
A nasa ɓangaren, Tinubu ya yaba wa jajircewarsa wajen tabbatar da dimukraɗiyya a ƙasar da kuma gudanar da lamuran zaɓe bisa gaskiya da adalci yayin da yake riƙe da muƙamin.
Kazalika, ya umarci Kwamishina mafi girma a hukumar, May Agbamuche-Mbu da ta karɓi muƙamin shugaba ta riƙo har zuwa lokacin da za a naɗa sabon shugaba a hukumar.
