
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Muryar Mata (VOW) ta karrama Gwamnatin Jihar Kaduna da kyautar gwarzuwar gwamnatin bisa tallafa wa mata da iyalansu.
An yi haka ne a babban taron ƙungiyar karo na 9 a Abuja, yau Talata.
Baya ga gwamnatin Kaduna, an kuam karrama gwamnatocin wasu jihohi da cibiyoyi duba da irin tasirinsu wajen inganta rayukan matata da walwalar iyalansu ta hanyar damawa da su a tsare-tsare da shirye-shirye.
Gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Uba Sani ta yi fice wajen nuna damuwa da lamarin kula da jinsi musamman wajen abinda ya shafi al’umma kai-tsaye da damawa da su a harkokin gwamnati.
Daga cikin shirye-shiryen da gwamnatin jihar ta samar akwai “Women Affirmative Procurement Policy, implementation of Gender Responsive Procurement” da kuma kafa ɓangaren kula da harkokin jinsi a ƙarƙashin Hukumar kula da kadarorin gwamnati ta jihar, KADPPA.
Haka kuma gwamnatin ta samar da tawagar kula da lamuran jinsi a KADPPA domin sanya ido wajen tabbatar da kiyayya dokoki da ƙa’idodi da suka shafi jinsi a ma’aikatu da hukumomi.
