Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mustapha Inuwa ya ce tun lokacin gwamnatin
Malam Umar Musa zuwa Aminu Bello Masari yake bada kwangila “amma ban taɓa yi da kaina ba ballantana ɗan wannan aikin,” Inji shi.
Dr Mustapha M Inuwa wanda tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina ne a lokacin gwamnatin marigayi Umaru Musa Yar’adua da RT Hon Aminu Bello Masari yayi wannan bayani kan zargin da ake masa na kwangilan ruwan Yantumaki da na Dam ɗin Karamar hukumar Ɗanmusa wanda ya ƙaryata hakan.
Wasu mutanen garin Ɗanmusa suke zarginsa da cewa gwamnatin baya ta bashi kwangilar aikin Dam ɗin Ɗanmusa da na Kawo ruwa cikin garin Yantumaki amma ya zuwa yanzu ba a kammala aikin ba.
Mustapha M. Inuwa ya faɗi cewa aikin Dam da samar da ruwan sha yazo ta hannun ɗan majalisar tarayya na Kaita da Jibiya akan ya bashi wuri da zai yi masa aiki a ƙaramar hukumar sa, dan nuna godiya akan irin halascin dake tsakanin su, a wancan lokacin.
Mustapha Inuwa wanda a yanzu madugun adawa ne a jam’iyar ADC a jihar yace,ya faɗawa ɗan majalisar tunda aikin ruwa ne aje Dam din Ɗanmusa ayi sai adawo cikin garin Yantumaki akawo musu wanda “ni da idona banga ɗan kwangilar ba, hakan yasa har Gwamna na wancan lokacin na faɗawa don ya ƙara yi mana godiya ba dan komai sai dan abun alkhairi ne aka mana a ƙaramar hukumar Ɗanmusa,”ya ce.
Sai ya shawarci masu zargin cewa yakamata su nemi wanda ya bada aikin shine ya kamata a tuntuɓa domin a ji meyasa aka bar aikin ko kuma dai ya fasa aikin ne “amma Mustapha Inuwa ba ɗan kwangila bane,”ya ce.
Ya bayyana yadda Sanata Ahmad Babba Kaita lokacin da yana kan kujerar Sanata ya tambaye shi yana so gina ɗakin karatu da samar da na’urar kwamfuta a Ɗanmusa “mu mukaje muka bashi wuri cikin makaranatar Yantumaki ya gudanar da wannan aikin kuma ba ɗan Ɗanmusa bane dan haka wannan aikin ba gwamnatin jiha ta bada shi ba, wani ne daga wata ƙaramar hukumar yazo zai yi kila kuma ya canza shawara akan haka,”inji Mustapha Inuwa.
“Kuma ai akwai tsohon shugaban ƙaramar hukumar Jibiya Bishir Maitan wanda yana cikin mutanen da suke gaba gaba wurin gudanar da aikin ko shi kuje ku nema ƙila yasan yadda aikin ya tsaya,”tsohon sakataren gwamnatin ya ce.
Sai dai Mustapha Inuwa ya ce yasan waɗanda suka sa ayi wannan da ya haka su suje su bincika yadda abun yake.
Sai wannan zarge zarge da ake yi masu sun musanta, a inda suke zargin wasu ne aka ɗauki nauyi domin su ɓata masu suna domin biyan buƙatar wasu.
