Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Uwar gidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Umar Raɗɗa, ta ƙaddamar da gangamin rigakafin cutar ƙyanda a Katsina, domin kare lafiyar yara a faɗin jihar.
Da take jawabi a wajen ƙaddamarwar, Hajiya Zulaihat ta bayyana cewa cutar kyanda na daga cikin manyan matsalolin lafiya da ke addabar yara a ƙasar nan, wadda ka iya janyo nakasa ko ma mutuwa.
Domin haka uwargidan Gwamnan ta yi kira ga iyaye maza da mata da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun karɓi wannan rigakafi domin inganta rayuwar su.”
Ta ƙara da cewa dukkan jihohin Najeriya za su gudanar da irin wannan gangami na rigakafi, inda a Jihar Katsina yara yan wata tara da haihuwa zuwa shekara goma sha hudu za su amfana.
Hajiya Zulaihat ta bayyana cewa rigakafin zai taimaka wajen kare yara sama da miliyan uku daga cututtuka kamar shan inna da cutar Kyanda, tana mai jaddada cewa rigakafin kyauta ne kuma yana da matuƙar muhimmanci.
“Ina kira ga iyaye da jama’a su yi amfani da wannan dama, su fito da ‘ya’yansu su karɓi allurar.
An kawo mana shi kyauta a nan Katsina. Don haka mu fito mu amfana da shi,” in ji ta.
Uwar gidan gwamnan ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da gangamin rigakafi a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar, inda ta roƙi matan shugabannin ƙananan hukumomi da masu hannu da shuni su bada goyon baya domin ganin nasarar shirin.
Hajiya Zulaihat ta yi godiya ga kwamishinan lafiya, hukumar lafiya matakin farko da sauran masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen kawo wannan shiri zuwa Katsina.
