“Na yi mamakin yadda littattafaina suka samu karɓuwa a sassan Nijeriya da Afirka”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Fatima Bala, wata marubuciya ce ýar Nijeriya da tauraronta ke haskawa, ba a Arewa kaɗai ba, har ma da wasu sassan Afirka. Kodayake rubutun da take yi da harshen Turanci ya fi mayar da hankali ne kan rayuwar ýan Arewa a Turai, musamman a ƙasar Kanada inda take zaune tare da iyalinta, amma muhimman darussan da take fitowa da su da suka shafi hukunce-hukuncen addini da tarbiyya, ya sa ta yi fice a tsakanin marubuta da manazarta a Nijeriya. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu ya samu damar zantawa da wannan marubuciya kuma malamar adabi, wacce ta bayyana masa ƙalubalen marubuta ýan Arewa da kuma muhimmancin tallafa wa marubuta mata. Ga yadda tattaunawar su ta kasance.
MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki. Wace ce Fatima Bala?
FATIMA: To, Salamu alaikum. Da farko dai kamar yadda ka faɗa sunana Fatima Bala. Ni marubuciyar littattafan labaran hikayoyi na Turanci ce. Sannan kuma ni malamar makaranta ce. Ina da aure da iyali.
Ki bamu tarihin rayuwarki a taƙaice?
Ni asalina ýar Jihar Kaduna ce. Na yi karatuna na firamare da sakandire duk a Kaduna. Kuma a halin yanzu ni malamar Jami’a ce, a ƙasar Kanada, inda nake zaune tare da iyalina.
Yaushe ki ka fara tunanin zama marubuciya?
A gaskiya ban taɓa tunanin watarana zan iya zama marubuciya ba, duk da yake tun tasowa ta na kasance mai sha’awar yawan karatun littattafai. Na fara rubutu ne a lokacin da aka yi zaman kulle na lokacin annobar Korona, a lokacin muna zaune a gida ba a fita aiki, sai dai mu yi daga gida. A sannan ne na fara gwada rubutun labari nawa na kaina, domin nishaɗi da ɗebe kewa, ba da tunanin zan fitar da shi a matsayin bugaggen littafi ba. Sai ga shi kuma Allah Ya ƙaddara cewa, zan zama marubuciya wacce har duniya ta san da ita.
Wanne labari ki ka fara rubutawa, kin buga shi ko tukunna?
Ba zan iya tuna sunan labarina na farko ba, don ban fitar da shi a matsayin littafi ba, sai dai na buga shi ne a zaurena na blog da nake saka rubuce-rubucena a wancan lokacin, a shekarar 2006. Kawo yanzu dai na fitar da littattafai guda uku, dukkan su da turanci na rubuta. Akwai littafin, ‘Before the Origin’, sai na biyu da na fitar mai suna ‘Broken: Not A Halal Love Story’, wanda a dalilin sa ne aka fara sanina a fagen rubutu. Sai kuma na ukun su littafin, ‘Hafsatu Bebi’. Yanzu haka kuma ina kan aikin wasu littattafan.
Sunanki ya fara tashe tun daga fitar littafinki na biyu, wanda aka fara sanin ki akai, wato ‘Broken’, mene ne sirrin samun ɗaukakarki?
To, a gaskiya babu wani sirri. Abin da zan ce kawai shi ne, daga Allah ne. Domin duk abin da ya faru, Allah ne Ya ƙaddara faruwarsa. Komai nawa na miƙa shi ne ga Allah Madaukakin Sarki. Kuma Alhamdulillahi, Yana amsa min.
Littafinki ya samu karɓuwa a wajen matasa a Arewacin Nijeriya, saboda yadda ki ka nuna kishin addini da al’ada a zamanance, me ya sa ki ka zaɓi wannan salo?
A matsayina ta Musulma ýar Arewa, ina ganin ya zama min dole in kare martabar addinina da al’ada ta. Kuma in yi amfani da baiwar da nake da ita in yaɗa koyarwar Musulunci da tarbiyyar rayuwar Hausawa. Saboda idan ban kare addinina ba, gobe idan wani ya yi rubutu ya ɓata sunan addinina, ba ni da bakin magana. Ina ganin wannan hakki ne na wajibi da ke kan kowanne Musulmi ɗan Arewa, musamman marubuta, da masu faɗa a ji, a kowanne ɓangare.
Akwai wasu muhimman darussa da ki ka kawo a cikin littattafanki biyu, waɗanda suka warware wasu batutuwa na addini, batun shayarwa daga mace guda da kuma aure tsakanin ýan’uwa na jini. Me ya sa ki ka zaɓi waɗannan jigo a rubutunki?
Shi ilimi ba ya ƙarewa a banza, abu ne mai daraja sosai. Na yi la’akari da cewa, ba kowa ne ya san matsayin koyarwar addinin Musulunci akan waɗannan matsaloli ba, don haka nake ganin ya zama hakki gare ni, na ilimantar da jama’a, a matsayin tunatarwa. A kullum idan ina rubutu, ina ƙoƙari in ga cewa, na sanya wasu darussa da jama’a za su koya daga rubutuna.
Yaya tasirin karɓuwar littattafanki in kin kwatanta da Arewacin Nijeriya da Kudanci, da kuma wasu sassan Afirka?
A gaskiya na yi mamakin yadda littattafaina suka samu karɓuwa a sauran sassan Nijeriya, da ma wasu ƙasashen Afirka. Da farko na yi tunanin ko littattafan za su fi tasiri ne kaɗai a Arewa saboda irin jigogin da nake rubutu a kansu, amma sai na lura ashe abin ba haka ba ne. Na yi mamaki ƙwarai da gaske, jin yadda littattafaina suka shiga wurare daban-daban, ba Nijeriya kaɗai ba. Ina da masoya littattafaina a Ghana Kenya, har zuwa Afirka ta Kudu.
Kin taɓa tunanin yin rubutu da Hausa, saboda Hausawa ýan Nijeriya, yankin da ki ka fito?
A gaskiya ba ni da ra’ayin yin rubutu da Hausa, na fi gane in yi da Turanci. Amma ba wai ina gudun Hausar ba ne sai dai na san akwai ƙwararrun marubuta a harshen Hausa, waɗanda suke ba da gudunmawa sosai a wannan ɓangaren. Sun kuma laƙanci harshen sosai da ƙa’idojin rubutunsa fiye da yadda ni zan yi. Don haka ina ganin babu abin da zan iya ƙarawa kan abin da suke yi.
Wanne ƙoƙari ki ke yi wajen nuna yadda rayuwar musulmi ýan Nijeriya take a ƙasar Kanada, da ƙalubalen cigaban zamani?
Ina ƙoƙarin bayyana yadda rayuwar Musulmin Nijeriya take a nan Kanada daidai gwargwado cikin gaskiya da adalci. Don nuna yadda tasirin rayuwa a ƙasashen Turai yake ga al’adu da zamantakewar ýan Afirka a nan. Amma a littafin da nake kan aiki a kansa yanzu ma na sauya akalar jigon labarin don ya duba yadda rayuwar ýan Arewa take a Nijeriya.
Wanne littafi ne wannan da ki ke kan rubutawa?
Wannan labarin da nake kan aikinsa yanzu haka yana da matuƙar muhimmanci a wurina, kuma ina fatan jama’a za su karɓe shi, kuma su ji daɗin sa idan ya fito.
Mun ga ɗaya daga cikin fitattun marubuta ýan Nijeriya dake waje, Chimamanda Ngozi Adichie, ta zo Nijeriya rangadi kan sabon littafinta, yaushe za mu sa ran ganin Fatima Bala?
In sha Allahu, nan ba da jimawa ba. Ina sa ran hakan.
Yaya alaƙar ki take da sauran marubuta na Nijeriya da ke wasu ƙasashen waje da ma na gida?
A gaskiya ina da kyakkyawar alaƙa tsakanina da sauran marubuta na Nijeriya, musamman waɗanda muke ƙarƙashin kamfanin ɗab’i na Masobe Books. Sun karɓe ni sosai, sun kuma nuna min kulawa. Na ji daɗin haka, kuma ina godiya ƙwarai da gaske.
Ta yaya matasa masu tasowa da ke sha’awar rubuce-rubuce za su iya samun nasara da gogewa?
Idan har sun yi haƙuri, kuma sun dage da rubutu, za su cimma nasara sosai. Lallai yana da kyau su dage da karatu, ba kawai karatu irin na labaran da suka fi sha’awa ba, su yi karatu sosai daga littattafai daban-daban. Kuma kada su ji kunya, su nemi shawara daga waɗanda suka gabace su. Domin kowa ma yana koyo ne daga wani.
Yaya ki ke ganin za a ƙarfafa gwiwar mata marubuta a Nijeriya da Afirka bakiɗaya, don su fito su nuna basirar su, musamman daga Arewa?
A ganina sai an bai wa mata marubuta dama da goyon baya, ta hanyar ƙara yawan tarukan baje-kolin littattafai da ƙara wa juna sani a harkar rubutun adabi a Arewa, da kuma yaɗa rubuce-rubucen su zuwa wurare daban-daban, musamman a zaurukan sada zumunta. Ina ganin idan ana ƙarfafa su, ana yayata ayyukan da suke yi, ta haka za a san su, har su ma su yi suna a ko’ina.
Labarin kowacce mace yana da daraja, kuma zai iya haskaka al’umma.
Mene ne ƙalubalen da ke gaban marubuta musulmi ýan Arewa?
A fahimta ta, manyan ƙalubalen da marubutan Arewa ke fuskanta, sun haɗa da sanin yadda za mu yi rubutu mai tsafta ba tare da saɓawa addini ba, da kuma nuna kyawawan al’adunmu cikin hikima yadda sauran al’umma za su fahimce mu, su kuma martaba mu. Wannan kuma yana buƙatar zurfafa tunani, amfani da hikima, cikin nuna gaskiya da adalci, da kare mutuncinmu.
Shin kina ganin ana samun kasuwar littattafan hikaya na turanci a Arewa kuwa?
Ana samu sosai ma kuwa!
Idan ba kya aiki, ko rubutu, wanne abu ne ya fi ɗebe miki kewa lokacin da ki ke hutawa?
Idan ba na aiki ko rubutu to, za ka same ni ina karatu. Idan kuma ba na karatu to, ina kallon finafinai. A gaskiya ina jin daɗin kallon finafinai sosai, a lokacin da nake hutawa cikin nishaɗi, musamman finafinan Indiya, ko namu na gida Nijeriya, na Turanci da na Hausa. Kamar Saira Movies, ina jin daɗin kallonsu sosai.
Na gode ƙwarai da gaske.
Ni ma ina matuƙar godiya.
