Ranar Malamai Ta Duniya: AUSUSS ta koka wa Gwamnan Kano

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/kudu

Ranar 5 ga watan Oktoba na kowacce shekara, ranace da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin murnar da yabawa malaman makarantu akan iri ƙoƙarin da suke yi wajen samar da illimi ga al’umma. Da nufin ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen tafiyar da sana’ar tasu domin samun al’umma ta gari.

Kazalika ranace da ake gudanar da bukukuwa da gabatar da jawabai kan wasu sabbin dabarun Koyarwa ko wata matsala, inda hukumomin illimi kan taro da jami’an gwamnati duk dan nunawa malaman muhimmanci wannan rana har ma da gabatar da wasu yan koke koken dan daukar matakin da ya dace.

Haka zalika, suma malaman da ƙungiyoyin su kan baje koli irin nasarorin da gwamnati ta samu a ɓangaren illimi dama yadda take kulawa dasu wajen samar musu da kayan aiki, biyan hakkokinsu domin inganta sana’ar ta su dan samun al’umma tagari. Sannan su gabatarwa da hukumomi wani koke ko gyara da ka iya kawo cigaban aikin nasu da nufin samawa ɗalibai illimi mai inganci.

A irin wannan rana ne itama ƙungiyar Malaman Makarantun Sakandire wato (ASUSS) reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Kwamared Usman Abdullahi Yalo ta gudanar da nata taron tare da duk membobin ƙungiyar da ke ƙananan hukumomin jihar 44 a ɗakin taro dake ɗakin karatu na Murtala Muhammad a birnin jihar.
A jawabinsa shugaban ƙungiyar yace maƙasudin shirya irin wannan taro a wannan rana shine, ranace da majalisar ɗinkin duniya ta ware domin su fito su faɗi irin nasarorin da suka samu da kalubalan da suka fuskanta dama mai kuma za a tunkara a shekara mai zuwa. Inda ya ƙara da cewa a dai wannan rana ne sukan haɗu da dukkan membobin ƙungiyar dake ko ina dan taya juna murnar wannan rana da kuma sada zumunci.

Yalo ya kuma bayyana gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamna mai kishin illimi duba da yadda yake bawa fannin muhimmanci idan akai la’akari da irin kason da yake warewa ɓangaren a kasafin kuɗin da yake gabatarwa a duk shekara. Wanda a cewarsa hakanne yasa jahar ta sami nasarar da ba a taɓa samun irin ta ba, inda jihar ta zo ta ɗaya a duk faɗin ƙasar nan wajen cin jarabawar NECO da WAEC ta bana da akayi, wanda hakan ya nuna irin jajircewa da gwamnan yake da ita wajan ganin yara sun sami illimi dan amfanar kansu dama al’ummar ƙasa.

Kwamared Yalo yaja hankalin malaman makarantun jihar da su jajirce wajen gudanar da aikin na su duba da yadda gwamnati ta tsaya wajen biya musu buƙatansu akan lokaci dan inganta rayuwarsu. Inda yace ya kama malaman su sakawa gwamnatin da alkhairi wajen ba wa yara ingantaccan Ilimi wanda za suyi gogayya a duk inda suka sami kansu.
A wani ɓangaren kuwa shugaban ƙungiyar Malaman Makarantun Sakandire, Kwamared Usman Abdullahi Yalo yayi riko tare da KUKAWA GWAMNAN Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf akan wasu matsaltsalinsu daya taimaka ya dawu musu da wasu alawus alawus wanda ada suna amfanarsu amman gwamnatin baya ta ceresu wanda basu san dalilinta na hakanba. Adam gane da hakanne yace sun miƙa kokon bararsu ga gwamnan da 7 ⁸ya taimaka yasa a cigaba da biyansu wannan alawus, domin hakan zai kara karfafawa malaman gwaiwa wajan gudanar da aikin nasu.
A nasa ɓangaran, Kwamashi nan Illimi na jihar Gwani Ali Haruna Makoda wanda ya sami wakilcen Darakta mai kula da ayyuka na musammam a ma’aikatar Malam Ashiru Muhammad taya malaman murnar wannan rana yayi tare da nuna godiya akan yadda suke kokarin bawa yara illimi da kuma tarbiya.
Inda yace gwamnati na iya bakin ƙoƙarinsa wajen samarwa da malamanai ababan more rayuwa da nufin suma su ringa walwala kamar sauran ma’aikata.
A nasa bayanin gwamnan jahar, Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda sakataren zartarwar hukumar kula da manyan makarantun sakandiran jahar da darakta mai kula da makarantu ya wakilta Malaman Abbas Abdullahi baya da taya su farin cikin ganin wannan rana da yayi yayi kira ga malaman dasu mayar da hankali kan aikin nasu domin sauki nauyin daya rataya a wuyansu na bawa yara illimi mai daukar da tarbiya.

Malam Abba yace zuwan wannan gwamnati ƙarkashin jagorancin gwamnan jihar an sami cigaba sosai.

By ukarofi