
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tshohon Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, Cif Uche Geoffrey Nnaji ya bayyana dalilan da suka sabbaba masa yin murabus daga muƙaminsa, inda ya ce ya yi haka ne don raɗin kansa ba saboda samun sa da laifi ba.
Ya bayyana cewa, ya zaɓi matakin ne domin girmama darajar doka da kare martabarta a daidai lokacin da aka zarge shi da amfani da takardun shaidar kammala karatun digiri da na NYSC na bogi.
A ranar Talata Nnaji ya fitar da saƙon murabus ɗin nasa daga muƙamin ministan bayan cecekuce ya ɓarke game da rashin tabbas na takardarsa ta digiri daga Jami’ar Nijeriya ta Nsukka (UNN) da kuma ta kammala NYSC.
Duk da cewa ya yi ikirarin kammala digirin farko a UNN a shekarar 1985, rahotanni sun bayyana cewa jami’ar ta gaza tantance shi a matsayin ɗaya daga cikin ƴaƴan da ta yaye, lamarin da ya janyo cecekuce da kushe acikin al’umma.
A wata takarda daga tsohon ministan, ya ce ya ajiye muƙamin ne domin girmama doka da janyewa daga zama matsala ga harkokin gwamnati.
Ya bayyana zargin a matsayin abinda aka siyasantar da nufin ɓata masa suna da ƙoƙarin cimma wata manufa da kuma raina hidima da gudumawar da ya bai wa ƙasa, yana mai cewa gaskiya za ta bayyana, sannan tarihi zai wanke mai gaskiya.
