Nijeriya ta sauka daga kan hanya – Hon Haruna Kadana

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU Kano

An bayyana cewa tsarin da shuwagabannin ƙasar nan na baya suka ɗora ƙasar ake an sauka daga kan hanya. Hakan ya fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar tsofaffan ‘yan takara na jam’iyar ADC na jihar Kano Hon Haruna Yahaya Kadana a yayin wani taron ƙungiyar da aka gabatar a ofishin jam’iyar.

Kadana yace babban dalilin su na shirya wannan taro a wannan lokacin domin taya ‘yan Najeriya murnar bikin ranar samun yancin kai na shekara 65 a wani ɓangaren kuma su gana da juna dan tattauna yadda jam’iyar ta su za ta sami nasara a zaɓe mai zuwa. “Mun shirya wannan taro ne don taya ‘yan ƙasa murnar ranar samun yancin kai da kuma ganawa da junanmu domin samun hanyar yadda jam’iyar mu za ta samu nasara a zaɓe mai zuwa in Allah ya kaimu”

Haruna Kadana ya ƙara da cewa dangane da murnar samun yancin kai kuwa ” ba za a ce ba a sami wani cigaba ba dan akwai cigaba a wasu ɓangarorin daban daban, amman dai ka duba yadda aka saka ƙasar nan magana ta gaskiya an sauka daga layi ina tabbatar maka da cewa ƙasar yadda shuwagabannin baya suka ɗora ta inda ace haka shuwagabannin yanzu suke tafi da ita to da wannan rashin tsarin ba zai wuce awa 24 ba, amman an bar komai ya lalace kalli ɓangaren illimi, lafiya kai komai ma baya tafiya dai dai .

Ya kuma bayyana shigowar irinsu tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Al-Rifa’i, tsohon gwamnan Ribas kuma tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyar LP Peter Obi da sauran manyan yan siyasar ƙasar nan da cewa wata babbar nasarace ga jam’iyar ta ADC wadda hakan zai iya zamai mata wata hanya ce ta cin zaɓe a shekara ta 2027.

A nasa jawabin shugaban jam’iyar na jihar Kano Alhaji Musa Shuaibu Ungogo cewa yayi baya ga murnar cikar Najeriya shekara 65 daga fita daga hannun turawan mulkin mallaka, sun gudanar da taron ne dan yan takarar da suka yiwa jam’iyar takara a muƙamai daban daban a shekarar zaben da ta gabata su gana da junansu.

Inda yace hakan zai taimakawa yan takarar su san cewa ƙungiyar tana nan kuma tana aikinta yadda ya kamata dan ganin an kai ga nasara a zaɓe mai zuwa domin ceto ƙasar nan daga halin da take ciki a yanzu.

Da yake nasa jawabin yayin taron, shugaban gamaiyar ƙungiyoyin haɗaka na jam’iyar ta ADC Hon Usama Galadima yace muhimmin haɗa wannan taron shine domin haɗa kan yan jam’iyar dama yan takarkarunsu waɗanda suka yi takara dama waɗanda suke da buƙatar tsayawa a nan gaba.

Daga nan ya ƙara da cewa samun yancin kai kuwa a ƙasar ba a sami wani cigaba ba domin har gwara ƙasar tana hannun turawan anfi samun cigaba idan aka kwatanta da halin da ake ciki a yanzu inda komai ya lalace. Inda ya bada tabbacin cewar da zarar jam’iyar ta ADC ta sami nasara to komai zai dawo dai dai a sami cigaban mai ɗorewa.

Ya kuma yi kira ga matasa da sauran alumma da su shigo sabuwar jam’iyar ta su domin itace kaɗai wadda za ta kawo gyara a ƙasar nan a sami cigaba da walwala.

Barista Maisara Abuyazid Aimais shine shugaban kwamatin horar da masu rabon katin zama ɗan jam’iyar na jihar Kano kira yayi ga yayan jam’iyar dama sauran al’umma da su fito domin su karɓi katin zama yan jam’iyar wanda sai dashi ne za su iya tsayawa takara a kowanne mataki. Maisara ya kuma ja hankalin al’ummar ƙasar nan da su tabbatar sun karɓi katin zaɓe wanda shine mataki na farko da za su iya kawo shugabannin da za su mayar da ƙasar nan kan hanya mai ɗorewa.

By ukarofi