Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU
Shugabar ƙaramar hukumar Tudun Wada Hajiya Sa’adatu Salisu ta ƙaddamar da aikin gina rijiyoyi 44 a mazaɓu 11 tare da kafa fitilun titi masu aiki da hasken rana.
Yayin duba waɗannan ayyukan raya ƙasa, Hajiya Sa’adatu wacce kuma ita ce Shugabar ƙungiyar shuwaganin ƙananan hukumomi ta Jihar Kano, ta bayyana cewa waɗannan ayyuka na daga cikin ƙudirin gwamnatinta na inganta ababen more rayuwa da samar da muhimman ayyukan al’umma.
Hakan na cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar ta Tudun wada Salisu Kassim Yakasai da ya rabawa manema labarai.
Shugabar ta ƙara jaddada cewa majalisar ƙaramar hukumar za ta ci gaba da mayar da hankali kan walwalar jama’a, musamman wajen tabbatar da samun tsaftataccen ruwan sha mai inganci.
Haka zalika ta miƙa godiya ga gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa bai wa ƙananan hukumomi damar gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa a yankunansu dan cigaban alummarsu.
A nasa jawabin, daraktan mulki da kuɗi Alhaji Ibrahim D. Haruna Bichi, ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da mara wa gwamnatin baya domin samun damar aiwatar da ƙarin muhimman ayyukan raya ƙasa masu amfani ga al’umma.
Alhaji Ibrahim ya bayyana cewa daga cikin rijiyoyi 44 da ake ginawa a mazaɓu 11, an riga an kammala rijiyoyi 34, sannan an rarraba fitilun titi masu amfani da hasken rana yadda ya dace, inda aka kammala matakin farko na aikin a cikin garin Tudun Wada.
