An naɗa Umar Usman Kibiya sarautar Ɗan Malikin Rano

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Mai martaba sarkin Rano Alhaji Dr. Muhammad Isa Umar (Autan Bawo) ya naɗa Alhaji Umar Usman Kibiya a matsayin sabon Ɗan Malikin Rano kuma ɗan majalisar sarki tare da wasu ƙarin mutane shida. Bikin naɗin wanda aka gudanar da shi a fadar Sarkin na Rano a ranar Juma’ar da ta gabata.

Dayake jawabi jim kaɗan bayan naɗin nasu, mai martaba sarkin na Rano yace majalisar tayi zurzurfan tunani tare da bincike a kan waɗanda aka naɗa sa’an nan aka zaɓo su. Ganin irin gudunmawar da suke bawa masarautar ta Rano tare da mazaunan yankin wanda ya haɗa da samarwa matasa aikin yin dan dogaro da kansu, tallafawa ɗalibai dan cigaban karatunsu, bunƙasa harkar kasuwanci domin cigaban yankin.

Sarkin ya ja hankalinsu da su ƙara jajircewa wajen taimakawa al’umma musammam marasa ƙarfi, inda yayi kira a garesu da su zamu jakadu na gari a duk inda suka sami kansu a nan gaba.

Da yake taya sabon Ɗan Malikin farin cikin wannan nadi, Mista Akaniyene Odoro wanda gudane daga cikin abokan karatunsa kuma ya zo ne daga jihar Akwa Ibom ya bayyana naɗin a matsayin abun burgewa wanda bai taɓa gani ba a zahiri face a kafafan yaɗa labarai ko ya karanta. Ya kuma bayyana Ɗan Malikin a matsayin mutumin kirki wanda tun lokacin suna makaranta bashi da wata matsala sannan mutum ne mai son zaman lafiya da kowa.

Shima wani makusancin nasa Alhaji Ibrahim Muazzam Abubakar ya taya Ɗan Malikin murnar wannan sabon matsayin da ya samu yana cewa wata babbar nasarace a rayuwarsa, tare da faɗin cewa abune da ya dace dashi ganin yadda yake tallafawa alumma da son zaman lafiya a duk inda yake ya kuma yi fatan alkhairi ga duk wanda su ka zo dan taya su murna.

Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Alhaji Musa Umar Kibiya a matsayin Baradan Rano, Alhaji Adamu Abdu Mato matsayin Gado da Masu, Dr Hadi Bala Bunkure shi kuma Sarkin Fadar Rano sai Alhaji Abba Ɗanlami Alhassan Talban Rano.
Sauran sun haɗa da Alhaji Umar Usman Kibiya wanda aka naɗa shi Ɗan Malikin Rano, Alhaji Abubakar Sarki a matsayin Ajiyan Rano da kuma Alhaji Adamu Yusuf Kibiya shi kuma Sadaukin Rano.

Bikin naɗin sarautun wanda aka gabatar a fadar mai martaba sarkin Rano Alhaji Muhammad Isa Umar ya sami halattar manyan sarakuna da hakiman masarautar ta Rano, manyan jami’an gwamnati, yan Kasuwa, yan siyasa na ciki da wajan Kano da ma sauran alumma.

By ukarofi