Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Nijeriya ta yi kira da a yi takatsantsan tsakanin matatar ɗangote da ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta ƙasa (PENGASSAN), tana mai cewa Nijeriya ta fi ƙarfin a tsayar da ita cak.
“Ba zai yiwu ba a tsayar da ƙasar nan cak saboda dambarwar ƙungiyar ma’aikata. Nijeriya gaba take da ƙungiyar PENGASSAN. Nijeriya sama take da kowannenmu,” mataimakin shugaban ƙasa ya jaddada a yayin bikin tattalin arziƙi na Nijeriya karo na 31 a Abuja a ranar Litinin.
“Wannan matatar an gina ta ne ta hanyar haɗakar zuba hannun jari da karɓar bashi daga bankuna na gida da na waje. Dole ne matatar ta yi aiki domin warware bashin da ke kanta, kuma ba zai yuwu ba a tsayar ƙasar nan cak saboda wata dambarwa da za a iya warwarewa cikin kwanciyar hankali,” ya faɗa.
Shettima yana wannan kalamai ne bayan wata dambarwa da ta ɓarke a watan da ya wuce bayan da matata mafi girma ta duniya ta sallami ma’aikatanta su 800 saboda zargin cin dunduniyar matatar da suka yi. Kamfanin ya ce, wannan al’amari ya kuma jawo damuwa game da kwanciyar hankali a yayin gudanar da ayyuka a matatar.
Wannan abu ya jawo yajin aiki wanda aka dakatar da shi a ranar Larabar da ta wuce wanda hakan ya jawo asarar man fetur ganga 200,000 a kowacce rana da kuma asarar biliyoyin nairori wanda kamfanin NNPC ya yi a ranar Litinin.
Shettima ya ce, Nijeriya za ta cigaba da ɗaukar matakai domin kare masana’antar mai da isakar gas da tabbatar da gudanar da ayyukansu yadda yakamata.
Mataimakin shugaban ƙasa ya yaba wa Aliko ɗangote, attajirin mafi arziƙi a nahiyar Afirka kuma mamallakin matatar man fetur ɗin saboda irin ƙoƙarin da ya yi wajen kafa matatar a Nijeriya a yayin da kamfanoni irinsa za su zaɓi zuba hannun jarinsu a wasu nau’o’in kasuwanci mafiya gwaɓi.
“Aliko Dangote, ba wai mutum ba ne kaɗai, shi kamfani wanda ke jan ragamar fatan da muke da shi na ganin bunƙasar tattalin arziƙin Nijeriya. Yadda muka mu’amalanci wannan bawan Allah, shi ne zai haska wa na wajen yadda za mu mu’amalance shi,” Shettuma ya faɗa.
Sannan ya ƙara da cewa, da a ce ya zuba hannun jarin Dala biliyan 10 a kamfanin Microsoft, ko Amazon ko Google, da zai yanzu kuɗinsa ya kai Dala biliyan 70 zuwa Dala biliyan 80.
“Amma ya zaɓi ya zuba jarinsa a ƙasarsa. Don haka akwai bashi da ke kan waɗanda za su zo nan gaba na karewa da alkinta wannan ƙasa mai albarka.”
