Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa fiye da ‘yan Nijeriya miliyan 33 na fuskantar matsanancin rashin abinci, yana mai cewa lamarin na buƙatar ɗaukar matakin gaggawa na doka.
Akpabio ya bayyana haka ne a zaman farko na Majalisar Dattawa bayan hutun shekara a Abuja, inda ya kuma jajanta wa jama’ar da ambaliyar ruwa ta shafa a jihohin Bayelsa, Sakkwato, da Zamfara.
Blueprint Manhaja ta rawaito cewa Akpabio ya ce yunwa ba za ta ƙare da magana kawai ba, sai da manufofi da kasafin kuɗi da ƙarfin zuciya, tare da buƙatar inganta noma da hanyoyin ƙauyuka da ban ruwa.
Shugaban majalisar ya kuma nuna damuwa kan ta’addanci da matsalar tsadar rayuwa, yana mai cewa jama’a na sa ran gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace wajen magance matsalolin.
Haka kuma, Akpabio ya bukaci a sake nazarin kundin tsarin mulki na 1999 domin ƙarfafa tsarin tarayya da dimokuraɗiyya, tare da kira ga haɗin kai tsakanin gwamnati ta tarayya da ta jihohi wajen dakile bala’o’in da ke addabar ƙasa.
