Kada ku jera shi da dillalan ƙwaya – Dangin Herbert Macaulay sun yi watsi da yafiyar Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dangin Marigayi Herbert Heelas Macaulay, sun yi watsi da salon da Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da shi wajen sanya sunan marigayin a jaddawalin dillalan ƙwaya da sauran masu manyan laifuka.

A wata hira da manema labarai a jihar Legas ranar Alhamis, mambobin iyalan Macaulay tare da Cif Olabode George, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa da Atona Oodua na ƙasar Yarabawa, sun bayyana rashin gamsuwa da abinda suka kira da sakacin gwamnati wajen kiyaye kima da darajar marigayin a idon al’umma, wanda ya faru sakamakon haɗa sunansa a waje ɗaya da na mutanen da suka karya dokokin ƙasa.

Yayin da suke yaba wa Shugaba Bola Tinubu wajen karrama gudumawar da Macaulay ya bayar ga ƴancin ƙasa da ci-gaban harkokin siyasa a Nijeriya, sun ce akwai buƙatar a karrama shi a keɓance kuma da mutuntawa ba wai a sa shi a sahun sauran mutane ba.

Cif George da dangin nasa sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta karrama shi ta hanyar sanya wa wata cibiya ko kadarar ƙasa sunansa akan hidimar da ya yi wa Nijeriya wanda ya kere na magabata da dama.

Sanannun ƴan dangin da suka halarci taron sun haɗa da Erelu Adeola Macaulay, Lanre Oshodi, Mayokun Thomas, Kofoworola Macaulay, Adeyinka Macaulay, Ayo Ogunlana da kuma Turi Akerele.

Da yake jawabi a taron, Cif George ya bayyana Herbert Macaulay a matsayin mutumin da ya haska hanyar samun ƴancin kai ga Nijeriya kuma wanda hangen nesansa ya zarce iya harkar siyasa.

By Babaji