Daga DAUDA USMAN a Legas
Daya daga cikin shugabannin manyan ɓangarorin kasuwar Mile 12 International Market da ke birnin Legas, Alhaji Mukhtar Jabo, wanda shi ne shugaban ɓangaren kasuwancin busasshen barkono, ya bayyana cewa su da sauran shugabannin sassa daban-daban na kasuwar suna ci gaba da gamsuwa da irin jagorancin da babban shugaban kasuwar, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam (Sardaunan Abeokuta), ke bayarwa.
Alhaji Mukhtar Jabo, ɗan asalin Jihar Jigawa kuma mazaunin unguwar Mile 12 a Legas, ya ce ba bu shakka cewa jagorancin Alhaji Shehu Samfam ya kawo sabuwar rayuwa da ci gaba a kasuwar Mile 12, wanda hakan ya jawo yabo daga ’yan kasuwa da al’umma baki ɗaya. A cewarsa, “Yabon gwani ya zama dole, domin idan aka kalli halin da kasuwar ke ciki a baya da kuma yadda take yanzu, babu shakka an samu gagarumin sauyi.”
Ya ƙara da cewa, a baya kasuwar ta cika da datti, babu tsarin tsabta, sannan gine-ginen shaguna sun kasance na ƙwanone masu sauƙin rushewa. Amma da zarar Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam ya hau mulki, sai aka soma babban gyara da tsaftacewar kasuwa gaba ɗaya, wanda ya sanya kasuwar ta zama cikin tsari da natsuwa.
Jabo ya bayyana cewa, “A yau, Mile 12 ta koma cikin tsari kamar kasuwannin ƙasashen Turai. Shaguna an sake gina su da bulo, an kafa tsarin jagoranci mai kyau, kuma kowanne bangaren kasuwanci yana da shugabansa, daga masu sauke kaya, masu rarraba kaya, dillalai, har zuwa iyayen kasuwa.”
Ya ce wannan tsarin jagoranci da Alhaji Shehu Samfam ya kafa ne ya haifar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin ’yan kasuwa, inda kowa yake da wakilci da damar bayyana matsayinsa cikin tsarin gudanarwa.
Alhaji Mukhtar Jabo ya ci gaba da cewa, “Kasuwar yanzu tana cikin ci gaba da gyara a kowane sashe. Wannan nasara ta samu ne saboda jajircewar shugabanmu, wanda ke kokarin ganin Mile 12 ta zama kasuwar zamani da ke kawo ci gaba ga ’yan kasuwa da tattalin arzikin Legas.”
Ya kuma yi kira ga Hausawa da sauran kabilu da ke gudanar da kasuwanci a Mile 12 da su ci gaba da goyon bayan shugabancin Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam domin tabbatar da dorewar wannan ci gaba.
A ƙarshe, Alhaji Jabo ya roƙi ’yan kasuwa su tashi tsaye wajen sabunta katin zabe (PVC) domin kare muradunsu a zabubbuka masu zuwa, tare da yin addu’ar fatan alheri da nasara ga shugabancin kasuwar da kuma zaman lafiya ga Nijeriya baki ɗaya.
