Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙarƙashin shirin “Urban Renewal” gwamnatin Katsina ta kashe fiye da Naira biliyan 113.51 wajen gina hanyoyi a manyan biranen Katsina, Funtua da Daura.
Hanyoyin sun ƙunshi gina EASTERN BYPASS da sha tale tale, tagwayen hanyoyi da gadoji, kwalbatoci da sanya fitillu masu amfani da hasken rana a titunan.
Darakta mai kula da aikin hanya na ma’aikatar ayyuka da gidaje na jihar Injiniya Falalu Hussaini ya shaidawa manema labarai haka a ofishin sa a Katsina.
Ya ce a Birnin Katsina kawai wanda itace babban birni, cikin wannan adadi, gwamnati ta kashe Naira biliyan 74.95 wajen gina hanyar EASTERN BYPASS da wasu tagwayen hanyoyi da sauran su masu tsawon kilomita 55.3.
Injiniya Falalu ya bayyana cewa aikin Kashi na ɗaya da na biyu duk an kammala su kuma har shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakin sa Sanata Kashim Shettima suka kaddamar a wata ziyarar aiki da suka kawo jihar.
Nan ma a garin Funtua gwamnatin Katsina ta kammala aikin tagwayen hanyoyi da shatale tale da sauran wasu manyan hanyoyi da ake sa ran kammala su kafin ƙarshen wannan shekara da kuma waɗanda za a kammala aikin a cikin shekara mai zuwa,”dukkan aikin hanyoyar gwamnati ta kashe Naira biliyan 19.2,”Inji injiniya Falalu.
A garin Daura kuwa gwamnati na shirin gina wani babban hanyar Shatale tale mai tsawon kilomita 14.43 da zai ci kuɗi Naira 19.55,ya ce.
Daraktan ya ce yanzu haka ma’aikatan ayyuka na jiran gwamnati ta kammala biyan diyya ga waɗanda aikin hanyar ya shafa domin su fara aiki.
“Kuma ana sa ran nan da watanni 14 za a kammala aikin hanyar,”inji
Falalu.
Ya ce gwamnati za ta kashe Naira biliyan 36.25 wajen kammala aikin hanyoyi masu tsawon kilomita 54.77 da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta gada daga gwamnatin baya.
Injiniya ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kashe biliyoyin kudi wajan samadda hanyoyi a wasu sassan jihar da suka haɗa kananan hukumomi da dama ha jihar.
