
Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe
Tsohon Shugaban ƙungiyar Matasa ta ƙasa reshen Jihar Gombe kuma Tsohon Shugaban Ƙungiyar Zabi Sonka da Taimakon Juna a jihar, Kwamared Garba Ubale, ya ci alwashin haɗe kan ƴaƴan ƙungiyar matuƙar aka zaɓe shi.
Ƴaƴan ƙungiyar daga yankin Arewa maso Gabas ne suka bayyana hakan a lokacin da suke zantawa da wakilinmu a shirye-shiryen ƙungiyar na zaɓenta na ƙasa.
Mambobin ƙungiyar daga sassa daban-daban na ƙasar suka nuna cikakken goyon baya ga Kwamared Garba Muhammad Ubale domin ya jagoranci ƙungiyar a matakin ƙasa.
Kwamared Garba, wanda ya shahara wajen shiryar da matasa da gina haɗin kai a tsakanin al’umma, ya taɓa zama Shugaban Majalisar Matasa ta Ƙasa (NYCN) reshen Jihar Gombe da kuma Shugaban Zabi Sonka a jihar. A cewar mambobi, shugabancinsa ya kasance abin misali na gaskiya, himma da sadaukarwa.
Sun ce, a ƙarƙashin jagorancinsa a Gombe, an gudanar da taron ƙasa na farko na ƙungiyar a shekarar 2009, wanda ya haɗa mambobi sama da 2,000 daga faɗin ƙasar.
Fiye da rabinsu ya sauke su da kuɗinsa na kansa, abin da ya tabbatar da kishinsa da jajircewarsa ga ci gaban ƙungiyar.
Da yake tsokaci kan manufofinsa, Kwamared Garba ya bayyana cewa idan ya samu damar jagoranci, zai mayar da hankali wajen sabunta tsarin ƙungiyar domin ta zama mai tasiri a fannonin aikin sa kai, tarbiyya da haɓaka kishin ƙasa tsakanin matasa.
Ya ce, ƙungiyar za ta sake fitowa fili a matsayin abin koyi ga sauran kungiyoyin matasa a Najeriya.
Ya kuma yi alkawarin haɗa kai da hukumomin gwamnati kamar Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA), Ma’aikatar Lafiya da Ma’aikatar Cigaban Matasa don ƙarfafa ayyukan ƙungiyar da shimfiɗa ta zuwa dukkan jihohi.
Ya ƙara da cewa zai yi aiki kafada da kafada da kafafen yaɗa labarai, musamman Radio Nigeria Kaduna da sauran gidajen rediyo a faɗin ƙasar, domin tallata shirye-shiryen ƙungiyar kamar aikin gayya da wayar da kan jama’a, tare da sabunta martabar ƙungiyar a matsayin ginshiƙin kishin ƙasa da hidimar al’umma.
