Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Sannunku da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja.
Idan kuna bibiye da mu za ku tuna a wancan mako mun faro shimfiɗa kan muhimmanci da amfanin darbejiya ga jiki. Kuma mun sanar da ku darasin bai ƙare ba, domin za mu kawo maku muhimmancin sa ga fata da yadda zai iya gyara ta.
A cikin duniyar mata ‘yan ƙwalisa, masu kula da kyau da lafiyar jiki, an daɗe ana yabon iccen darbejiya, wato neem tree, a matsayin ɗaya daga cikin kyautukan da Allah ya ba wa fatar jikin mace. Wannan icce, wanda ake kira “dokin magani” a wurin masana, ya kasance cike da sinadarai masu warkarwa da kuma inganta fata ta kowanne yanayi, wato ba na wucen gadi ba kamar yadda wasu mayuka ke yi ba.
Shafin Kwalliya zai yi duba zuwa ga yadda darbejiya ke zama amintacciyar abokiyar mace wajen kula da garan fata.
1. Tsaftace fata daga datti da ƙwayoyin cututtuka:
Fatar mutum, musamman a yankunan da ake yawan zufa ko ƙura, na buƙatar tsafta ta musamman. Ruwan ganyen darbejiya na da ƙarfi wajen kashe ƙwayoyin cututtuka da suke haddasa kuraje.
Idan ana shafa ruwan dafaffen ganyensa kullum a fuska ko jiki, yana taimakawa wajen kawar da datti da kuma hana kumburi.
Hanyar amfani:
A tafasa ganyen darbejiya ka bari ya huce, sannan a goge fuska da ruwan da auduga sau biyu a rana. Fatar za ta fara nuna tsabta da santsi cikin kwanaki kaɗan.
2. Maganin ƙuraje da rage man fuska:
Masana kula da fata sun tabbatar da cewa oil ɗin darbejiya (Neem oil) yana da ikon rage yawan mai da fata ke fitarwa. Haka kuma yana warkar da kurajen da suka riga suka bayyana ta hanyar busar da su cikin natsuwa ba tare da barin tabo ba.
Amfani:
A gauraya ɗan neem oil (kaɗan) da zuma ko aloe vera, a shafa a fuska na mintuna 15 kafin a wanke. Wannan sinadari yana da ƙarfin rage kumburin fata.
Za mu ci gaba.
