Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Har yanzu alkalamina na kan wasu ‘yan bazata da ke biyowa ta bayan gida don yin maƙarƙshiya ga zaman lafiya a tsohon Lardin Arewacin Nijeriya. Hakika duk Lardi na da iyaye har ma da kakanni da mutanen kirki ke alfahari da girmama su. A ɓangaren waɗannan ‘yan bazata na Arewa aibanta shugabannin da su ke da amfani da labaru na shaci-faɗi da murɗe wuyan tarihi don cimma miyagun muradunsu. Duk mai yawo a dandalin yanar gizo da ya shafi Arewa zai ci karo da waɗannan mutanen da akasarinsu matasa ne. Ba lallai dukkansu na cikin Nijeriya ba, wasu na ƙasashen ƙetare inda daga kan su ke cillo gubar da ta ke illa ga zamantakewar al’ummar Arewa.
In ban da jahilci da rashin sanin duniya yaya mutum zai rubuta – I AM HAUSA ACITIVIST!? Duk duniya a yi ta rankatakaf ba mai alaƙanta “activism” da kunna wutar ƙabilanci. Wannan gwagwarmaya ta “activism” ba aikin ƙabilanci ta ke nufi ba a’a sam, amma ta na nufin aiki ga dukkan al’umma don kawo canji kamar yanda Malam Aminu Kano ya yi. Su Malam Sa’adu Zungur da rubutun wake, irin su lauya Gani Fawehinmi, ’Yar aikin mishan Baturiya Mary Salessor da ta yaƙi kashe jarirai a Okoyong, Kuros Riba. Matakin ƙetare ga su ‘yan gurguzu Karl Maɗ, Vladimir Lenin, irin su Chiyaman Mao a ƙasar Sin, Nelson Mandela da ya yaki wariyar launin fata a Afurka ta kudu, Ga Martin Luther King da ya rasa ran sa don tabbatar da adalci tsakanin farare da baƙaƙe a Amurka, Fidel Castro a Cuba da sauran su da dama. Wadannan duk ’yan gwagwarmaya ne da ba su da tsoron kamu balle ɗauri. Sun yi aiki lokacin da ba ma irin wannan ‘yanci na faɗar ra’ayi. Mandela sai da ya shafe shekara 27 a daure kafin gwagwarmayar sa ta yi nasara. To amma wani baubawan burmi da wayar salula a boye a wani ɗaki ya yi iƙirarin wai shi “activist” ne kuma ba a san ko shi waye ba ne ba hoto ba sunan gaskiya sai aikin ruruta wutar ƙabilanci a zamanin da ba na jahiliyya ba.
Duniya ta kawo mu zamanin da matashi da ciiko a kan sa ya zo ya na iƙirarin wai gwagwarmaya ya ke yi ta ceto al’ummar mu daga zalunci. ‘Yan kwangilar rusa Arewa haka su ke. Ko a wajen sa kaya daga ‘yan ƙalilan da su ka bar hotunan su za ka ga kare ne da fatar akuya. Ko ‘yar babbar riga su ka saka za ka ga ba lallai ta bi lafiyar jikin su ba don kasancewar ba a saba ba. Kai balle ma wani ya yi karambanin saka hula nan za ka gane kifa kwando a ka yi don kan dama kwaryar molo ne an saba shan rana ba a tashi da tarbiyyar Malam Bahaushe ba. Makalewa da sanya hotunan wasu shugabannin kasa ko wasu alamu a matsayin shaidar hoto ta buɗe shafukan su na makirci ya ɓoye gano haƙiƙanin yanda mutanen su ke. Ai na taɓa haska aƙalla hotunan wasunsu da su ka yi kama da mashaya giya ga goshi ba annurin nafila ba na sallar walaha. Gaskiyar magana mafi takarkarewa a cikin makiran nan ba su da alaka ta nesa ko ta kusa da Hausawa, hasalima makiya Hausawa ne da ke ramuwa kan abun da su ke gani hana su sakat da addinin Islama ya yi daga tsafe-tsafe, rawar banjo, yankawa dodo zabbi da buɗe mayankar naman kare 404.
Akwai waɗanda a ka tinkara da karɓar wannan kwangilar ta rusa Arewa amma Allah ya haska mu su makiricin su ka zulle don ai ba mai hankalin da za a mikawa ashana a ce ƙona rumbunan garin ku ka kawo tokar a saya da tsada. Mai karɓar irin wannan kwangila sai ɗan banza 7 na haƙiƙa ba na tarihin da wasu ke ruwaitowa ba. Cikin mutanen nan fa wani ma da na’ura ya ke amfani wajen samun fassarar Hausa sai ya riƙa cilla makaman makirci har ya wuce makaɗi da rawa don rashin sanin al’adun Hausawa. Gane al’adun Hausawa da iya aikata su daidai sai dan gado amma wanda ya yi haye ta soshiyal midiya kan fallasa kan sa wajen nuna ai ba bambanci tsakanin Musulmin mu da waɗanda ba Musulmi ba da ma ‘yan gargajiya. Kai ni na ga wanda ya dauka madugun addinin tsafi Barbushe na Tsumburbura na da daraja don haka a ajiye Musulunci a koma harkar matsafa na zamanin jahiliyya.
Abun da ke ƙarfafa min gwiwa kamar yanda sam-sam ba mai iya raba hanta da jini hakanan ba mai iya raba Bahaushe da addinin Musulunci don kururuwar shaidan ta ƙabilanci. Gaskiya ne an yaudari wasu ƙalilan a matasan mu na Arewa sun biyewa wannan makircin da tunanin yakin karɓar ‘yanci ne amma wannan duk sai a yanar gizo ba sakaran da zai fito bakin kasuwa a arewacin Arewa ya ɗau amsa kuwwa ya tallata wannan farafagandar ko ya sha giyar wake ne. Ir wani ya fito ma na a Gusau, Sokoto Birnin Kebbi ko a cikin Badala a Kano ko Babban Dodo a Zaria ya zagi Shehu Mujaddadi, Sir Ahmadu Bello ko ya shiga Gwammaja ya na cewa an yi amfani da Malam Aminu ne don bautar da ‘yan NEPU ya gani ko ƙafar sa za ta kai shi. Ina ‘yan gwagwarmayar karya ku gwada ma na in da gaske ku ke yi. Wallahi abun da ya sa mu ke haska mutanen nan ba wai don sun kai a yi maganar su ba ne, zamanin yau na wayar salula ne inda in ka yi sake ka na tarbiyyatar da mutanen gidanka waya na warwarewa! Haba in da zamanin da ba wayar salula da kafofin yanar gizo ne ai ni ma da sai na ajiye alƙalami na a ragaya.
Haƙiƙa in makiran nan za su fito su yi magana, tsamin harshen su na garma-garmar Hausa da ma waɗanda ko zo in kashe ba ba su iya ba; ba mai sayan su sisin koɓo. Allah ya tsari gatari da saran shuka. Ba a bun da ya fi zama lafiya a kasa. Duk inda a ka samu ɓarkewar fitina to ba wani abun alheri da zai iya gudana. Gwamnati ta na yaƙar ‘yan ta’adda a kowane ɓangare da ya sanya jami’an tsaro ke neman goyon bayan jama’a don cimma nasara. A yayin da a ke wannan himmar, ba daidai ba ne wasu kuma su ɓullo da wata hanyar haddasa mafi munin fitina da za ta iya barazana ga ɗaukacin ƙasar. Lallai aiki ne ga duk mai kishin kasa ya yaki duk wata manufa ta tada fitina a ƙasa kama daga dalilan siyasa, bambancin addini, yanki ko fakewa da ƙabilanci.
KAMMALAWA
A ƙasar nan akwai ƙungiyoyin Musulmi akwai na Kirista sannan akwai inda a ke addinin gargajiya. Kowa na da hurumin yin addinin da ya kwanta ma sa a rai. Fakewa da ‘yan ta’addan daji don cimma ɓoyayyiyar manufa ba za ta samu nasara ba. Aikin gwamnati ne murƙushe duk wanda ke kawo fitina a kasa kuma mun ga yanda gwamnati ta murƙushe ‘yan awaren Biyafara a yakin basasa, mun ga yanda a ka murkushe Marwa Maitatsine a Kano, mun ga yadda a ke cigaba da fafutukar kakkaɓe ‘yan boko haram a Arewa maso gabar, yanzu kuma ga ɓarayin daji ga Lakurawa da a ke cigaba da ɗaukar matakan magance su. Mazauna jihohin da kalubalen ya fi shafa ne mafi haƙƙin bayyana halin da a ke ciki. Baya ga dakarun gwamnatin tarayya, Gwamnan Zamfara Dauda Lawal Dare da Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda duk sun ɗauki askarawan sa-kai da ke artabu da ‘yan ta’addan. An hallaka da yawa daga cikin su da ma jagororin su irin su Halliru Sububu, Kachalla Ali, Baleri da ma can baya Buharin Daji da ‘yan ta’addan su ka kashe.
Shawara ta a nan ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya CAN ta tsawatawa duk Kiristan da zai saurare ta wanda ke zagin manyan shugabannin Musulmi da wadanda su ka jajirce wajen krabo ‘yanci daga Turawna mulkin mallaka, ya daina don tabbas in fitinar kabilancin nan da makiran nan ke rurawa ta kama bal-bal ba wanda zai tsira. Makiyan Nijeriya daga ƙetare, ba addini ya dame su ba, burinsu, su ga Nijeriya ta wargaje. Idan ta wargaje kuwa ba wani shugaban addini da zai sake tasiri in ma ya tsira sai a sansanin ‘yan gudun hijira. Shin wane sansani ne zai wadaci zaman ‘yan Najeriya miliyoyi ko ma a takaice kan ‘yan Arewa? Girman Arewa da tasirinta ya sa duk abun da ya shafe ta to sai ya girgiza dukkan kasa. Mu ƙaddara yankin Arewa ne ke neman ballewa daga Nijeriya shin me mu ke tsammani zai samu ƙasar. Allah ya kiyaye.
Shawara ga malaman Islama su shiga wayar da kan jama’a don fahimtar miyagun irin nan da jagorantar addu’o’in Allah ya wargaza makircinsu.
Na tabbata gwamnati na bin wannan kunna wutar sabuwar fitina kuma ina da kwarin guiwa da yardar Allah nan gaba kadan saura ƙiris jami’an tsaro za su cafke jagororin wannan farafaganda ‘yan ƙalilan na bayyane da masu yawa da ke tsammanin rufe shafukan bayanan su, ya tserar da su daga bankaɗowa! Bakauyen birni ba ya gane ya taka kaya sai ya ji ankwa a hannunsa.
