
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.
A yau Alhamis aka yi taron rantsarwar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Hakan na zuwa ne makonni kaɗan da wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu ya ƙare a muƙamin.
A makon da ya gabata ne Majalisar Dattawa ta tabbatar da Amupitan a matsayin sabon shugaban INEC bayan tantance shi da kuma zaɓen baka daga ƴan majalisa.
Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo ne da iyalan Amupitan da wasu manyan ƙasa suka mara masa baya a yayin taron rantsarwar.
Da yake jawabi, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yaba wa iyalan Amupitan da masu yi masa fatan alheri da suka samu halartar taron, yana mai cewa ya tsallake dukkan jarrabawar tantancewar da aka masa da fatan sauke nauyinsa bisa aminci.
